Shelar Almasihu Gicciyeyye
1 Sa’ad da na zo wurinku, ‘yan’uwa, ban zo ina sanar da ku asiran Allah ta wurin iya magana ko gwada hikima ba.
2 Don na ƙudura a raina, sa’ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye.
3 Ina kuma tare da ku ne da rauni, da tsoro, da rawar jiki ƙwarai.
4 Jawabina da wa’azina, ba su danganta ga maganar rarrashi ko ta wayo ba, sai dai ga rinjaye na ikon Ruhu,
5 kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.
Bayani daga Ruhun Allah
6 Duk da haka dai muna sanar da hikima ga waɗanda suka kammala, sai dai ba hikimar wannan zamani ba, ba kuwa ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda suke shuɗewa ba.
7 Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu.
8 A cikin masu mulkin zamanin nan, ba wanda ya gane hikimar nan, don da sun gane ta, da ba su gicciye Ubangiji Maɗaukaki ba.
9 Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,
“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,
Kunne bai taɓa ji ba,
Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,
Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”
10 mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al’amuran Allah.
11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.
12 Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake.
13 Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al’amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.
14 Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na’am da al’amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.
15 Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome, shi kansa kuma ba mai jarraba shi.
16 “Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.