Kada Ka Ɗora wa Ɗan’uwanka Laifi
1 A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra’ayinsa ba.
2 Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.
3 To, kada fa mai cin kome ɗin nan yă raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan, yă ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu.
4 Kai wane ne har da za ka ga laifin baran wani? Ko dai ya tsaya, ko ya faɗi, ai, ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
5 Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna a cikin haƙƙaƙewa, a kan ra’ayinsa.
6 Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.
7 Duk a cikinmu ba wanda ya isar wa kansa a sha’anin rayuwarsa ko mutuwarsa.
8 Ko muna a raye, zaman Ubangiji muke yi, ko mun mutu ma, zaman Ubangiji muke yi. Ashe, ko muna a raye, ko kuma a mace, na Ubangiji ne mu.
9 Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sāke rayuwa, wato, domin ya zama shi ne Ubangijin matattu da na rayayyu duka.
10 To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan’uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan’uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari’ar Allah.
11 Domin a rubuce yake,
“Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini,
Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”
12 Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.
Kada Ka Sa Ɗan’uwanka Yin Tuntuɓe
13 Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan’uwansa,
14 Na sani, na kuma tabbata, a tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake marar tsarki ga asalinsa, sai dai ga wanda ya ɗauke shi marar tsarki ne yake marar tsarki.
15 In kuwa cimarka tana cutar ɗan’uwanka, ashe, ba zaman ƙauna kake yi ba. Kada fa cimarka ta hallaka wannan da Almasihu ya mutu dominsa.
16 Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.
17 Ai, Mulkin Allah ba ga al’amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
18 Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.
19 Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.
20 Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.
21 Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan’uwanku yin tuntuɓe.
22 Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne.
23 Wanda yake shakka, amma kuwa ya ci, ya sani ya yi laifi ke nan, domin ba da bangaskiya ya ci ba. Duk abin da ba na bangaskiya ba ne, zunubi ne.