Allah Ya Zaɓi Isra’ila
1 Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,
2 cewa ina da matuƙar baƙin ciki da kuma takaici marar yankewa a zuciyata.
3 Da ma a la’ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, ‘yan’uwana na kabila!
4 Su ne Isra’ilawa. Da zama ‘ya’yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari’a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.
5 Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.
6 Ba cewa Maganar Allah ta fādi ba, don ba duk zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ilawa na gaske ba.
7 Ba kuwa duk su ne ‘ya’yan Ibrahim ba, wai don suna zuriyarsa. Amma an ce, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.”
8 Wato, zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ‘ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.
9 Alkawarin kuwa shi ne, “Baɗi war haka zan dawo, Saratu kuma za ta haifi ɗa.”
10 Banda haka ma, sa’ad da Rifkatu ta yi ciki da mutumin nan ɗaya, wato, kakanmu Ishaku,
11 tun ba ta haifi ‘ya’yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau–don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa–
12 aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.”
13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”
14 To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a’a, ko kusa!
15 Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.”
16 Ashe kuwa, abin bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
17 Don a Nassi an ce da Fir’auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”
18 Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.
19 Kila ka ce mini, “To, don me har yanzu yake ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
20 Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”
21 Ashe, maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata domin aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya?
22 To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka,
23 Nufinsa ne yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka?
24 Wato, mu ke nan da ya kira, ba kuwa daga cikin Yahudawa kaɗai ba, har ma daga cikin al’ummai.
25 Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Yusha’u cewa,
“Waɗanda dā ba jama’ata ba,
Zan ce da su ‘jama’ata,’
Wadda dā ba abar ƙaunata ba kuma,
Zan ce da ita ‘abar ƙaunata.’ ”
26 “A daidai wurin da aka ce da su, ‘Ku ba jama’ata ba ne,’
A nan ne za a kira su ‘’ya’yan Allah Rayayye,’ ”
27 A game da Isra’ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto.
28 Domin Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi ɗaya.”
29 Kamar yadda Ishaya ya yi faɗa cewa,
“Da ba domin Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba,
Da mun zama kamar Saduma,
An kuma maishe mu kamar Gwamrata.”
Isra’ila da Bishara
30 To, me kuma za mu ce? Ga shi, al’ummai da ba su nace da neman adalcin Allah ba, sun samu, wato, sun sami adalcin da yake daga bangaskiya.
31 Isra’ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta.
32 Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen tuntuɓe,
33 kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Ga shi, na sa dutsen sa tuntuɓe a Sihiyona,
Da fā na sa faɗuwa.
Duk mai gaskatawa da shi, ba zai kunyata ba.”