Bulus a Tsibirin Malita
1 Bayan da muka tsira, sai muka ji, ashe, sunan tsibirin nan Malita ne.
2 Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.
3 Sa’ad da Bulus ya tattaro waɗansu ƙirare rungume guda ya sa a wutar, sai ga wani maciji ya bullo saboda zafi, ya ɗafe masa a hannu.
4 Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”
5 Bulus kuwa ya karkaɗe ƙwaron a cikin wutar, bai kuwa ji wani ciwo ba.
6 Su kuwa suna zaton wurin zai kumbura, ko kuwa farat ɗaya ya fāɗi matacce. Amma da aka daɗe suka ga ba abin da ya same shi, suka sāke magana suka ce lalle shi wani Allah ne.
7 A nan kusa kuwa akwai wani fili, mallakar shugaban tsibirin nan, mai suna Babiliyas. Shi ne ya karɓe mu, ya sauke mu a cikin martaba har kwana uku.
8 Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu’a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.
9 Da aka yi haka sai duk sauran marasa lafiya a tsibirin suka riƙa zuwa ana warkar da su.
10 Suka yi mana kyauta mai yawa, da za mu tashi a jirgin ruwa kuma, suka yi ta tara mana duk irin abubuwan da muke bukata.
Bulus Ya Isa Roma
11 Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.
12 Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.
13 Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.
14 A nan muka tarar da waɗansu ‘yan’uwa, suka roƙe mu mu kwana bakwai tare da su. Da haka dai har muka isa Roma.
15 Da ‘yan’uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.
16 Da muka shiga Roma aka yardar wa Bulus ya je ya sauka abinsa tare da sojan da yake tsaronsa.
Wa’azin Bulus a Roma
17 Bayan kwana uku ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “Ya ku ‘yan’uwa, ko da yake ban yi wa jama’armu wani laifi ba, ko laifi a game da al’adun kakanninmu, duk da haka an bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima.
18 Su kuwa da suka tuhume ni, suna so su sake ni, don ban yi wani laifi da ya isa kisa ba.
19 Amma da Yahudawa suka ƙi yarda, sai ya zamar mini dole in nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar, ba don ina ƙarar jama’armu ba ne.
20 Shi ya sa na nema in gana da ku, tun da yake dai saboda sa zuciyar nan da Isra’ila take yi ne nake ɗaure da sarƙan nan.”
21 Sai suka ce masa, “Mu kam, ba mu sami wata wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, ba kuwa wani ɗan’uwanmu da ya zo nan ya kawo labarinka, ko yă faɗi wata mummunar magana game da kai.
22 Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra’ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko’ina ana kushenta.”
23 Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa’an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.
24 Waɗansu sun rinjayu da maganarsa, amma waɗansu sun ƙi gaskatawa.
25 Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,
26 ‘Je ka wurin jama’ar nan, ka ce,
Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,
Za ku gani kuma, amma ba za ku gane ba faufau.
27 Don zuciyar jama’ar nan ta yi kanta,
Sun toshe kunnuwansu,
Sun kuma runtse idanunsu,
Wai don kada su gani da idanunsu,
Su kuma ji da kunnuwansu,
Su kuma fahimta a zuciyarsu,
Har su juyo gare ni in warkar da su.’
28 To, sai ku sani, wannan ceto na Allah, an aiko da shi har ga al’ummai, su kam za su saurara.”
29 (Da ya faɗi haka, sai Yahudawa suka tashi suna ta muhawwara da juna.)
30 Sai Bulus ya zauna a nan a gidan da yake haya, har shekara biyu cikakku, yana maraba da duk wanda ya je wurinsa,
31 yana ta wa’azin Mulkin Allah, da koyar da al’amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.