Bulus Ya Ɗaukaka Ƙara zuwa ga Kaisar
1 To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.
2 Sai manyan firistoci da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi
3 ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya ‘yan kwanto su kashe shi a hanya.
4 Amma Festas ya amsa ya ce, “Bulus yana a tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.”
5 Ya kuma ce, “Saboda haka, sai waɗansu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”
6 Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari’a, ya yi umarni a zo da Bulus.
7 Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.
8 Amma Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari’ar Yahudawa, ko Haikali, ko a game da Kaisar ba, ko kaɗan.”
9 Festas kuwa don neman farin jini wurin Yahudawa, ya amsa ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?”
10 Amma Bulus ya ce, “Ai, a tsaye nake a majalisar Kaisar, a inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wa Yahudawa wani laifi ba, kai kanka kuwa ka san da haka sarai.
11 To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai, ba zan guji a kashe ni ba, amma in ba wata gaskiya a cikin ƙarata da suke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don a faranta musu rai. Na nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.”
12 Bayan da Festas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”
Bulus a gaban Agaribas da Barniki
13 Bayan ‘yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.
14 Da yake kuma sun yi kwanaki da dama a can, sai Festas ya rattaba wa sarki labarin Bulus, ya ce, “Akwai wani mutumin da Filikus ya bari a ɗaure,
15 wanda sa’ad da nake Urushalima manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙararsa, suka roƙe ni in yi masa hukunci.
16 Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al’adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari’a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.
17 Saboda haka, da suka zo nan tare, ban yi wani jinkiri ba, sai kawai na hau gadon shari’a kashegari, na kuma yi umarni a kawo mutumin.
18 Da masu ƙarar suka tashi tsaye, ba su kawo wata mummunar ƙara yadda na zata a game da shi ba,
19 sai dai waɗansu maganganu da suka ɗora masa a game da addininsu, da kuma wani, wai shi Yesu, wanda ya mutu, amma Bulus ya tsaya a kan, wai yana da rai.
20 Ni kuwa da na rasa yadda zan bincika waɗannan abubuwa, sai na tambayi Bulus ko ya yarda ya je Urushalima a yi masa shari’a a can a kan waɗannan abubuwa.
21 Amma da Bulus ya nema a dakatar da maganarsa sai Augustas ya duba ta, sai na yi umarni a tsare shi har kafin in aika da shi zuwa gun Kaisar.”
22 Sai Agaribas ya ce wa Festas, “Ni ma dai na so in saurari mutumin nan da kaina.” Festas ya ce, “Kā kuwa ji shi gobe.”
23 To, kashegari sai Agaribas da Barniki suka zo a cikin alfarma, suka shiga ɗakin majalisa tare da shugabannin yaƙi da kuma jigajigan garin. Sai aka shigo da Bulus da umarnin Festas.
24 Sai Festas ya ce, “Ya sarki Agaribas, da dukan mutanen da suke tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama’ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu, bai kamata a bar shi da rai ba.
25 Amma ni ban ga abin da ya yi wanda ya isa kisa ba. Tun da kuma shi kansa ya nema a mai da shari’arsa a gaban Augustas, ƙudura in aika da shi zuwa wurinsa.
26 Amma ba ni da wata tabbatacciyar magana da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku, musamman kuwa a gabanka, ya sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na abin da zan rubuta.
27 Don ni, a ganina, wauta ce a aika da ɗan sarƙa, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”