Bulus Ya Koma Makidoniya da Hellas
1 Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.
2 Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa masu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas,
3 ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa’ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.
4 Subataras Babiriye, ɗan Burus, shi ya raka shi, tare da Aristarkus da Sakundas, mutanen Tasalonika, da Gayus Badarbe, da Timoti, har ma da Tikikus da Tarofimas, mutanen Asiya,
5 waɗanda suka riga tafiya suka jira mu a Taruwasa.
6 Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan idin abinci marar yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna har kwana bakwai.
Taruwar Bankwana a Taruwasa
7 A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura gurasa, Bulus ya yi masu jawabi, don ya yi niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakar dare.
8 Akwai kuwa fitilu da yawa a benen da muka taru.
9 Da wani saurayi a zaune a kan taga, mai suna Aftikos, sai barci ya ci ƙarfinsa sa’ad da Bulus yake ta tsawaita jawabi, da barci mai nauyi ya kwashe shi, sai ya faɗo daga can hawa na uku, aka ɗauke shi matacce.
10 Amma Bulus ya sauka ƙasa, ya miƙe a kansa, ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, ai, yana da rai.”
11 Da Bulus ya koma sama, ya gutsuttsura gurasa ya ci, ya daɗe yana magana da su, har gari ya waye, sa’an nan ya tashi.
12 Sai suka tafi da saurayin nan a raye, daɗin da suka ji kuwa ba kaɗan ba ne.
Tafiya a Teku daga Taruwasa zuwa Militas
13 Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin, muka miƙe sai Asus da nufin ɗaukar Bulus daga can, don dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyyar bi ta ƙasa.
14 Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini.
15 Daga nan kuma muna tafe a jirgin ruwan dai, kashegari kuma sai ga mu daura da tsibirin Kiyos. Kashegari kuma, ga mu a tsibirin Samas, kashegari kuma sai Militas.
16 Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.
Bulus Ya Yi wa Dattawan Ikkilisiyar Afisa Jawabi
17 Daga Militas ne ya aika Afisa a kira masa dattawan Ikkilisiya.
18 Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku, tun ran da na sa ƙafata a ƙasar Asiya,
19 ina bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u, har da hawaye, da gwaggwarmaya iri iri da na sha game da makircin Yahudawa.
20 Kun kuma san yadda ban ji nauyin sanar da ku kowane abu mai amfani ba, ina koya muku a sarari, da kuma gida gida,
21 ina tabbatar wa Yahudawa da al’ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.
22 To, ga shi kuma, yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu yana iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,
23 sai dai Ruhu Mai Tsarki yakan riƙa tabbatar mini a kowane gari, cewa ɗauri da shan wuya na dākona.
24 Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
25 To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.
26 Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,
27 domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.
28 Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.
29 Na sani bayan tashina waɗansu mugayen kyarketai za su shigo a cikinku, ba kuwa za su ji tausayin garken ba.
30 Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.
31 Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.
32 To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.
33 Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani.
34 Ku da kanku kun sani hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda suke tare da ni.
35 Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
36 Da Bulus ya faɗi haka, ya durƙusa, duka suka yi addu’a tare.
37 Sai duk suka fashe da kuka, suka rungume Bulus, suna ta sumbantarsa,
38 suna baƙin ciki tun ba ma saboda maganar da ya faɗa ba, cewa ba za su ƙara ganinsa ba. Daga nan suka rako shi har bakin jirgi.