Majalisar Ikkilisiyar Urushalima
1 Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa ‘yan’uwa, suna cewa, “In ba an yi muku kaciya kamar yadda al’adar Musa take ba, ba dama ku sami ceto.”
2 A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawwara Bulus da Barnaba suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansunsu, su je Urushalima gun manzanni da dattawan Ikkilisiya a kan wannan magana.
3 To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al’ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan ‘yan’uwa ƙwarai.
4 Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.
5 Amma waɗansu masu ba da gaskiya, ‘yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari’ar Musa.”
6 Sai manzannin da dattawan Ikkilisiya suka taru su duba maganar.
7 Bayan an yi ta muhawwara da gaske, Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya ‘yan’uwa, kun sani tun farkon al’amari, Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne al’ummai za su ji maganar bishara, su ba da gaskiya.
8 Allah kuwa, masanin zuciyar kowa, ya yi musu shaida da ya ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
9 Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.
10 Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?
11 Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12 Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa’ad da suke ba da labarin mu’ujizai da abubuwan al’ajabi, da Allah ya yi ga al’ummai ta wurinsu.
13 Bayan sun gama jawabi, Yakubu ya amsa ya ce, “Ya ku ‘yan’uwa, ku saurare ni.
14 Bitrus ya ba da labari yadda Allah ya fara kula da al’ummai, domin ya keɓe wata jama’a daga cikinsu ta zama tasa.
15 Wannan kuwa daidai yake da maganar annabawa, yadda yake a rubuce cewa,
16 ‘Bayan haka kuma zan komo,
In sāke gina gidan Dawuda da ya rushe,
In sāke ta da kangonsa,
In tsai da shi,
17 Domin sauran mutane su nemi Ubangiji,
Wato al’umman da suke nawa.’
18 Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.
19 Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah,
20 sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.
21 Domin tun zamanin dā, a kowane gari akwai masu yin wa’azi da littattafan Musa, ana kuma karanta su a majami’u kowace Asabar.”
Amsar Majalisar Ikkilisiya
22 Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan ‘yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin ‘yan’uwa,
23 da wannan takarda cewa, “Daga ‘yan’uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga ‘yan’uwanmu na al’ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.
24 Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikinmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da yake ba mu umarce su da haka ba,
25 sai muka ga ya kyautu, da yake bakinmu ya zo ɗaya, mu aiko muku waɗansu zaɓaɓɓun mutane, tare da ƙaunatattunmu Barnaba da Bulus,
26 waɗanda suka sayar da ransu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu.
27 Don haka, ga shi, mun aiko muku Yahuza da Sila, su ma za su gaya muku waɗannan abubuwa da bakinsu.
28 Domin Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da suke wajibi, wato
29 ku guji abin da aka yanka wa gunki, da cin nama tare da jini, da cin abin da aka maƙure, da kuma fasikanci. In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya. Wassalam.”
30 Su kuma da aka sallame su, suka tafi Antakiya, da suka tara jama’ar, suka ba da wasiƙar.
31 Da suka karanta ta, suka yi farin ciki saboda gargaɗin.
32 Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi ‘yan’uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.
33 Bayan sun yi ‘yan kwanaki a wurin, sai ‘yan’uwa su sallame su lafiya, suka koma wurin waɗanda suka aiko su.
34 [Amma Sila ya ga ya kyautu shi ya zauna a nan.]
35 Bulus da Barnaba kuwa suka dakata a Antakiya, suna koyarwa suna kuma yin bisharar Maganar Ubangiji, tare da waɗansu ma da yawa.
Bulus ya Rabu da Barnaba
36 An jima, Bulus ya ce wa Barnaba, “Bari yanzu mu koma mu dubo ‘yan’uwa a kowane gari da muka sanar da Maganar Ubangiji, mu ga yadda suke.”
37 Barnaba kuwa ya so su tafi da Yahaya, wanda ake kira Markus.
38 Amma Bulus bai ga ya kyautu su tafi da wanda ya rabu da su a ƙasar Bamfiliya, ya ƙi tafiya aiki tare da su ba.
39 Sai matsanancin saɓanin ra’ayi ya auku, har ya kai su ga rabuwa. Barnaba ya ɗauki Markus, suka shiga jirgin ruwa zuwa tsibirin Kubrus,
40 amma Bulus ya zaɓi Sila, bayan ‘yan’uwa sun yi masa addu’a alherin Allah ya kiyaye shi, ya tafi.
41 Bulus ya zazzaga ƙasar Suriya da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa Ikilisiyoyi.