Misali na wadda Mijinta Ya Mutu da Alƙali
1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu’a, kada kuma su karai.
2 Ya ce, “A wani gari an yi wani alƙali marar tsoron Allah, marar kula da mutane.
3 A garin nan kuwa da wata wadda mijinta ya mutu, sai ta riƙa zuwa wurinsa, tana ce masa, ‘Ka shiga tsakanina da abokin gābana.’
4 Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,
5 amma saboda gwauruwar nan ta dame ni, sai in bi mata hakkinta, don kada ta gajishe ni da yawan zuwa.’ ”
6 Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan marar gaskiya ya faɗa!
7 Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?
8 Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa’ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”
Misali na Bafarisiye da Mai Karɓar Haraji
9 Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,
10 “Waɗansu mutum biyu suka shiga Haikali yin addu’a, ɗaya Bafarisiye, ɗaya kuma mai karɓar haraji.
11 Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu’a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.
12 Duk mako ina azumi sau biyu. Kome na samu nakan fitar da zakka.’
13 Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’
14 Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”
Yesu Ya sa wa ‘Yan Yara Albarka
15 Waɗansu suka kawo masa ‘yan yaransu domin ya taɓa su. Ganin haka sai almajiransa suka kwaɓe su.
16 Amma Yesu ya kira ‘yan yara wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai, Mulkin Allah na irinsu ne.
17 Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na’am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”
Shugaban Jama’a Mai Arziki
18 Wani shugaban jama’a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”
19 Sai Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Ai, ba wani Managarci, sai Allah kaɗai.
20 Kā dai san umarnan nan, ‘Kada ka yi zina. Kada ka yi kisankai. Kada ka yi sata. Kada ka yi shaidar zur. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
21 Sai ya ce, “Ai, duk na kiyaye waɗannan tun ƙuruciyata.”
22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”
23 Da jin haka, sai ya yi baƙin ciki gaya, don shi mai arziki ne da gaske.
24 Yesu kuwa da ya gan shi haka, ya ce, “Kai! Da ƙyar kamar me masu dukiya su shiga Mulkin Allah!
25 Ai, zai fiye wa raƙumi sauƙi ya bi ta kafar allura, da mai arziki ya shiga Mulkin Allah.”
26 Waɗanda suka ji wannan magana suka ce, “To, in haka ne, wa zai sami ceto ke nan?”
27 Amma Yesu ya ce, “Abin da ya fi ƙarfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28 Sai Bitrus ya ce, “To, ai, ga shi, mun bar mallakarmu, mun bi ka.”
29 Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko ‘yan’uwansa, ko iyayensa, ko kuma ‘ya’yansa, saboda Mulkin Allah,
30 sa’an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”
Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi
31 Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata.
32 Gama za a bāshe shi ga al’ummai, a yi masa ba’a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.
33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”
34 Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.
Warkar da Makaho Mai Bara a kusa da Yariko
35 Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara.
36 Da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko mene ne.
37 Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne yake wucewa.”
38 Sai ya ɗaga murya ya ce, “Ya Yesu Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”
39 Sai waɗanda suke gaba suka kwaɓe shi ya yi shiru. Amma ƙara ɗaga murya yake yi ƙwarai da gaske, yana cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayina!”
40 Sai Yesu ya tsaya, ya yi umarni a kawo shi wurinsa. Da ya zo kusa, ya tambaye shi,
41 “Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ya Ubangiji, in sami gani!”
42 Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
43 Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama’a suka yabi Allah.