W. YAH 6

Hatiman

1 To, ina gani sa’ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”

2 Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.

3 Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”

4 Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.

5 Da ya ɓamɓare hatimi na uku, na ji rayayyiyar halittar nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa.

6 Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha’ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”

7 Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu ta ce, “Zo.”

8 Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu’in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.

9 Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.

10 Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”

11 Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, ‘yan’uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.

12 Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,

13 taurari kuma suka faɗa a ƙasa kamar yadda ɓaure yake zubar da ɗanyun ‘ya’yansa, in ƙasaitacciyar iska ta kaɗa shi,

14 sararin sama ya dāre ya naɗe kamar tabarma, sai aka kawar da kowane dutse, da kowane tsibiri daga mazauninsa.

15 Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma’arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,

16 suna ce wa duwatsun, “Ku faɗo a kanmu, ku ɓoye mu daga idon wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma fushin Ɗan Ragon nan,

17 don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”