LUK 9

Yesu ya Aiki Goma Sha Biyu ɗin Nan

1 Sai ya tara goma sha biyun nan ya ba su iko da izini kan dukan aljannu, su kuma warkar da cuce-cuce,

2 ya kuma aike su su yi wa’azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.

3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.

4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.

5 Duk waɗanda ba su yi na’am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”

6 Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko’ina.

Mutuwar Yahaya Maibaftisma

7 To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.

8 Waɗansu kuwa suka ce wai Iliya ne ya bayyana. Waɗansu kuma suka ce ɗaya daga annabawan dā ne ya tashi.

9 Sai Hirudus ya ce, “Yahaya kam na fille masa kai. Wa ke nan kuma da nake jin irin waɗannan abubuwa game da shi?” Sai ya nemi ganinsa.

Ciyar da Mutum Dubu Biyar

10 Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Betsaida.

11 Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.

12 Da rana ta fara sunkuyawa, sha biyun suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda muke ba mutane.”

13 Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama’an nan abinci ne.”

14 Maza sun yi wajen dubu biyar. Sai ya ce wa almajiransa, “Ku ce musu su zazzauna ƙungiya ƙungiya, kowace ƙungiya misali hamsin hamsin.”

15 Haka kuwa suka yi, suka sa dukkansu su zazzauna.

16 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama’a.

17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.

Hurcin Bitrus a kan Yesu

18 Wata rana yana addu’a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?”

19 Suka amsa suka ce, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.”

20 Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.”

Yesu Ya Faɗi irin Mutuwar da zai Yi

21 Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana.

22 Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”

23 Sai ya ce wa dukansu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, yă bi ni.

24 Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, tattalinsa ya yi.

25 Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a kan hasarar ransa, ko a bakin ransa?

26 Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa’ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala’iku tsarkaka.

27 Amma hakika ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Mulkin Allah.”

Sākewar Kamanninsa

28 Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu’a.

29 Yana yin addu’a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.

30 Sai ga mutum biyu na magana da shi, wato Musa da Iliya.

31 Sun bayyana da ɗaukaka, suna zancen ƙaura tasa ne, wadda yake gabannin yi a Urushalima.

32 Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.

33 Mutanen nan na rabuwa da shi ke nan, sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Maigida, ya kyautu da muke nan wurin. Mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” Bai ma san abin da yake faɗa ba.

34 Yana faɗar haka sai wani gajimare ya zo ya rufe su. Da kuma gajimaren ya lulluɓe su suka tsorata.

35 Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!”

36 Bayan muryar ta yi magana, aka ga Yesu shi kaɗai. Suka yi shiru. A kwanakin nan kuwa ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Farfadiya

37 Kashegari da suka gangaro daga kan dutsen, wani babban taro ya tarye shi.

38 Sai ga wani daga cikin taron ya yi kira, ya ce, “Malam, ina roƙonka ka dubi ɗana da idon rahama, shi ne ke nan gare ni.

39 Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.

40 Na kuwa roƙi almajiranka su fitar da shi, amma sun kasa.”

41 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”

42 Yana zuwa, sai aljanin ya buge shi ƙwarai, jikinsa na rawa. Amma Yesu ya tsawata wa baƙin aljanin, ya warkar da yaron, ya kuma mayar wa ubansa da shi.

43 Duk aka yi mamakin girman ikon Allah.

Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da zai Yi

Tun dukansu suna mamakin duk abubuwan da yake yi, sai ya ce wa almajiransa,

44 “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

45 Amma ba su fahimci maganan nan ba, an kuwa ɓoye musu ita ne don kada su gane. Su kuwa suna tsoron tambayarsa wannan magana.

Wane ne Mafi Girma?

46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.

47 Amma da Yesu ya gane tunanin zuciyarsu, ya kama hannun wani ƙaramin yaro ya ajiye shi kusa da shi.

48 Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”

Wanda ba ya Gāba da ku, Naku Ne

49 Sai Yahaya ya amsa ya ce, “Maigida, mun ga wani yana fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.”

50 Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Samariyawan wani Ƙauye sun Ƙi Karɓar Yesu

51 Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.

52 Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.

53 Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.

54 Da almajiransa Yakubu da Yahaya suka ga haka suka ce, “Ya Ubangiji, ko kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama ta lashe su?”

55 Amma ya juya, ya tsawata musu.

56 Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.

Masu Cewa za su Bi Yesu

57 Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”

58 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

59 Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”

60 Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne ‘yan’uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”

61 Wani kuma ya ce, “Ya Ubangiji, zan bi ka, amma ka bar ni tukuna in yi wa mutanen gida bankwana.”

62 Yesu ya ce masa “Wanda ya fara huɗa da keken noma, yana duban baya, bai dace da Mulkin Allah ba.”