MAR 7

Al’adun Shugabanni

1 To, da Farisiyawa suka taru a wurinsa tare da waɗansu daga cikin malaman Attaura da suka zo daga Urushalima,

2 suka lura waɗansu almajiransa na cin abinci da hannuwa marasa tsarki, wato marasa wanki.

3 Domin Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, saboda bin al’adun shugabanninsu.

4 In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu al’adu da yawa da suka gada suke kiyayewa, kamar su wankin ƙore, da tuluna, da daruna.

5 Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun shugabanni, sai su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsarki?”

6 Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa,

‘Al’umman nan a baka kawai suke girmama ni,

Amma a zuci nesa suke da ni.

7 A banza suke bauta mini,

Domin ƙa’idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’

8 Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al’adun mutane.”

9 Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al’adunku!

10 Domin Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ da kuma, ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa, sai lalle a kashe shi.’

11 Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),

12 shi ke nan fa, ba saura ku bar shi ya yi wa ubansa ko uwa tasa aikin kome.

13 Ta haka kuke banzanta Maganar Allah ta wajen al’adunku na gargajiya. Kun kuwa cika yin irin waɗannan abubuwa.”

Abubuwan da Suke Ƙazantarwa

14 Sai ya sāke kiran jama’a, yă ce musu, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimta.

15 Ba abin da yake shiga mutum daga waje yă ƙazanta shi, sai abin da yake fita, yake ƙazanta shi. [

16 Duk mai kunnen ji, yă ji.]”

17 Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi ma’anar misalin.

18 Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahimta ne? Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi,

19 tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.

20 Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazanta shi.

21 Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,

22 da kwaɗayi, da mugunta, da ha’inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.

23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kuwa ƙazanta mutum.”

Bangaskiyar Mata Basurofinikiya

24 Daga nan kuma ya tashi ya tafi wajajen Taya da Sidon. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa ya sani ba, amma ba ya ɓoyuwa.

25 Nan da nan sai wata mace, wadda ‘ya tata ƙarama take da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta fāɗi a gabansa.

26 Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa ‘ya tata da aljanin.

27 Yesu ya ce mata, “Bari ‘ya’ya su ƙoshi tukuna, domin bai kyautu a bai wa karnuka abincinsu ba.”

28 Amma ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin ‘ya’ya.”

29 Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da ‘yarki.”

30 Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

Yesu Ya Warkar da Bebe

31 Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.

32 Suka kawo masa wani kurma mai i’ina, suka roƙe shi ya ɗora masa hannu.

33 Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwansa, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshensa.

34 Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”

35 Sai aka buɗe kunnuwansa, aka saki kwaɗon harshensa, ya kuma yi magana sosai.

36 Yesu ya kwaɓe su kada su faɗa wa kowa, amma ƙara yawan kwaɓonsu ƙara yawan yaɗa labarin.

37 Suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har kurma ma ya sa ya ji, bebe kuma ya yi magana.”