Warkar da Mai Aljan na Garasinawa
1 Suka iso hayin teku a ƙasar Garasinawa.
2 Da saukarsa daga jirgin, sai ga wani mai baƙin aljan daga makabarta ya tarye shi.
3 Shi kuwa makabarta ce mazauninsa. Ba mai iya ɗaure shi kuma, ko da sarƙa ma.
4 Don dā an sha ɗaure shi da mari da sarƙa, amma ya tsintsinka sarƙar, ya gutsuntsuna marin, har ma ba mai iya bi da shi.
5 Kullum kuwa dare da rana yana cikin makabarta, da kan duwatsu, yana ta ihu, yana kukkuje jikinsa da duwatsu.
6 Da dai ya hango Yesu, sai ya sheƙo a guje ya fāɗi a gabansa,
7 ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.”
8 Ya faɗi haka ne domin Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!”
9 Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.”
10 Sai ya roƙi Yesu da gaske kada ya kore su daga ƙasar.
11 To, wurin nan kuwa da wani babban garken alade na kiwo a gangaren dutsen.
12 Aljannun nan suka roƙe shi suke ce, “Tura mu wajen aladun nan, mu shiga su.”
13 Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka halaka a ruwa.
14 Daga nan sai ‘yan kiwon aladen suka gudu, suka ba da labari birni da ƙauye. Jama’a suka zo su ga abin da ya auku.
15 Da suka zo wurin Yesu suka ga mai aljannun nan a zaune, saye da tufa, cikin hankalinsa kuma, wato mai aljannun nan masu yawa a dā, sai suka tsorata.
16 Waɗanda aka yi abin a kan idonsu kuwa, suka farfaɗi abin da ya gudana ga mai aljannun da kuma aladen.
17 Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu.
18 Yana shiga jirgi ke nan, sai mai aljannun nan a dā ya roƙe shi izinin zama a gunsa.
19 Amma Yesu bai yardar masa ba, ya ce masa, “Tafi gida wurin ‘yan’uwanka, ka faɗa musu irin manyan abubuwan da Ubangiji ya yi maka, da kuma yadda ya ji tausayinka.”
20 Sai ya tafi, ya shiga baza labari a Dikafolis na irin manyan abubuwan da Yesu ya yi masa. Duk mutane kuwa suka yi al’ajabi.
Warkar da ‘Yar Yayirus da Matar da ta Taɓa Gezar Mayafin Yesu
21 Da Yesu ya sāke haye ƙetare cikin jirgi, sai babban taro ya kewaye shi. Shi kuwa yana bakin tekun.
22 Sai ga wani daga cikin shugabannin majami’a, mai suna Yayirus. Da ganin Yesu kuwa ya fāɗi a gabansa,
23 ya roƙe shi da gaske, yana cewa, “’Yata ƙaramar tana bakin mutuwa. Idan dai a ce ka zo ka ɗora mata hannu, sai ta warke ta rayu.”
24 Sai suka tafi tare. Babban taro kuwa na biye da shi, suna matsa tasa.
25 Sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini,
26 ta kuma sha wahala da gaske a hannun masu magani da yawa, har ta ɓad da duk abin da take da shi, amma duk a banza, sai ma gaba-gaba cutar take yi.
27 Da ta ji labarin Yesu, ta raɓo ta bayansa cikin taron, ta taɓa mayafinsa.
28 Don tā ce a ranta, “Ko da tufarsa ma na taɓa, sai in warke.”
29 Nan take zubar jininta ta tsaya, ta kuma ji a jikinta an warkar da cutarta.
30 Nan da nan kuwa da Yesu ya ji wani iko ya fita daga gare shi, sai ya waiwaya a cikin taron, ya ce, “Wa ya taɓa tufata?”
31 Sai almajiransa suka ce masa, “Kana ganin taro na matsarka, ka ce, wa ya taɓa ka?”
32 Sai Yesu ya juya domin ya ga wadda ta yi haka.
33 Matar kuwa da ta san abin da aka yi mata, sai ta zo a tsorace, tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta faɗa masa ƙashin gaskiya.
34 Sai ya ce mata, “’Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”
35 Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami’a suka ce, “Ai, ‘yarka ta rasu, me kuma za ka wahalar da Malamin?”
36 Amma Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, ya ce wa shugaban majami’a, “kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai.”
37 Bai bar kowa ya bi shi ba sai Bitrus, da Yakubu, da kuma Yahaya ɗan’uwan Yakubu.
38 Da suka isa gidan shugaban majami’a, ya ji ana hayaniya, ana kuka, ana kururuwa ba ji ba gani.
39 Da kuma ya shiga, ya ce musu, “Don me kuke hayaniya kuna kuka haka? Ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.”
40 Sai suka yi masa dariyar raini. Shi kuma bayan ya fitar da su duka waje, sai ya ɗauki uban yarinyar, da uwa tata, da kuma waɗanda suke tare da shi, ya shiga inda yarinyar take.
41 Ya kama hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi”, wato, “Ke yarinya, ina ce miki, tashi.”
42 Nan take yarinyar ta tashi ta yi tafiya, domin ‘yar shekara goma sha biyu ce. Nan da nan kuwa mamaki ya kama su.
43 Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.