Yesu Ya Warkar da Shanyayye
1 Bayan ‘yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida.
2 Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa’azin Maganar Allah.
3 Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi.
4 Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai.
5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.”
6 To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciya tasu,
7 suna cewa, “Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake! Wa yake da ikon gafarta zunubi banda Allah kaɗai?”
8 Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?
9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta maka zunubanka’, ko kuwa a ce, ‘Tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka yi tafiya’?
10 Amma don ku sakankance Ɗan Mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–
11 “Na ce maka, tashi ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
12 Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”
Kiran Lawi
13 Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama’a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.
14 Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
15 Wata rana Yesu yana cin abinci a gidan Lawi, masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa kuma suna ci tare da shi da almajiransa, don kuwa da yawa daga cikinsu masu binsa ne;
16 to, da malaman Attaura na Farisiyawa suka ga yana cin abinci tare da masu zunubi da masu karɓar haraji, suka ce wa almajiransa, “Don me yake ci yake sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
17 Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”
Tambaya a kan Azumi
18 To, almajiran Yahaya da na Farisiyawa suna azumi, sai aka zo aka ce masa, “Don me almajiran Yahaya da na Farisiyawa suke azumi, amma naka almajirai ba sa yi?”
19 Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.
20 Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.
21 Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.
22 Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasara tasa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi, ai sai sababbin salkuna.”
Almajirai na Zagar Alkama Ran Asabar
23 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, suna cikin tafiya sai almajiransa suka fara zagar alkamar.
24 Farisiyawa suka ce masa, “Ka ga! Don me suke yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba?”
25 Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da ya matsu da yunwa, shi da abokan tafiyarsa?
26 Yadda ya shiga masujadar Allah a zamanin Abiyata babban firist, ya ci keɓaɓɓiyar gurasan nan, wadda bai halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai, har ma ya ba abokan tafiyarsa?”
27 Sai ya ce musu, “Ai, Asabar domin mutum aka yi ta, ba mutum aka yi domin Asabar ba.
28 Saboda haka Ɗan Mutum shi ne Ubangijin har da na ranar Asabar ma.”