Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu
1 Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,
2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su.
3 Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”
4 An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
5 “Ku ce wa ‘yar Sihiyona,
Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,
Mai tawali’u ne,
Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6 Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu.
7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau.
8 Yawancin jama’a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya.
9 Taron jama’a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”
10 Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”
11 Sai jama’a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”
Yesu Ya Tsabtace Haikalin
12 Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin ‘yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.
13 Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu’a,’ amma ku kun maishe shi kogon ‘yan fashi.”
14 Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.
15 Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al’ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.
16 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,
‘Kai ne ka shiryar da ‘yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”
17 Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.
La’antar da Itacen Ɓaure
18 Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.
19 Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin ‘ya’ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.
20 Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?”
21 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.
22 Kome kuka roƙa da addu’a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”
Ana Shakkar Izinin Yesu
23 Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”
24 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan.
25 To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
26 In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.”
27 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
Misali na Mai ‘Ya’ya Biyu Maza
28 “To, me kuka gani? An yi wani mutun mai ‘ya’ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’
29 Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi.
30 Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba.
31 To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.
32 Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi
33 “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata ‘yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa’an nan ya tafi wata ƙasa.
34 Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.
35 Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.
36 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.
37 Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’
38 Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’
39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.
40 To, sa’ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”
41 Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,
‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al’ajabi ne.’
43 Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al’umma wadda za ta ba da amfani nagari.
44 Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake.
46 Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama’a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.