Mutuwar Yahaya Maibaftisma
1 A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.
2 Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu’ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”
3 Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan’uwansa Filibus.
4 Don dā ma Yahaya ya ce masa bai halatta ya zauna da ita ba.
5 Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama’a, don sun ɗauka shi annabi ne.
6 To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai ‘yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,
7 har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa.
8 Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”
9 Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.
10 Ya aika aka fille wa Yahaya kai a kurkuku,
11 aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwa tasa.
12 Almajiransa suka zo suka ɗauki gangar jikin, suka binne, suka kuma je suka gaya wa Yesu.
Ciyar da Mutum Dubu Biyar
13 Da Yesu ya ji haka sai ya tashi daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, domin ya kaɗaita. Amma da taron jama’a suka ji haka, suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.
14 Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.
15 Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”
16 Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.”
17 Sai suka ce masa, “Ai, gurasa biyar da kifi biyu kawai muke da su a nan.”
18 Sai ya ce, “Ku kawo mini su.”
19 Sa’an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama’a.
20 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.
21 Waɗanda suka ci kuwa misalin maza dubu biyar ne banda mata da yara.
Yesu Yana Tafiya a kan Ruwan Teku
22 Sai ya sa almajiransa suka shiga jirgi su riga shi hayewa kafin ya sallami taron.
23 Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu’a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai.
24 Sa’an nan kuwa jirgin yana tsakiyar teku, raƙuman ruwa mangara tasa, gama iska tana gāba da su.
25 Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.
26 Sa’ad da kuwa almajiran suka gan shi yana tafiya a kan ruwan, sai suka firgita suka ce, “Fatalwa ce!” Suka yi kururuwa don tsoro.
27 Sai nan da nan ya yi musu magana ya ce, “Ba kome, Ni ne, kada ku ji tsoro.”
28 Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, in kai ne, to, ka umarce ni in zo gare ka a kan ruwan.”
29 Ya ce, “Zo mana.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin, ya taka ruwa ya nufi gun Yesu.
30 Amma da ya ga iska ta yi ƙarfi sai ya ji tsoro. Da ya fara nutsewa sai ya yi kururuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”
31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
32 Da shigarsu jirgin iska ta kwanta.
33 Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”
Yesu Ya Warkar da Marasa Lafiya a Janisarata
34 Da suka haye, suka sauka a ƙasar Janisarata.
35 Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka aika ko’ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya,
36 suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, iyakar waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.