MAT 13

Misali da Mai Shuka

1 A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.

2 Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.

3 Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka.

4 Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.

5 Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.

6 Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.

7 Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su.

8 Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.

9 Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Manufar Misalan

10 Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?”

11 Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.

12 Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

13 Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.

14 Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,

‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,

Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,

15 Don zuciyar jama’ar nan ta yi kanta,

Sun toshe kunnuwansu,

Sun kuma runtse idanunsu,

Don kada su gani da idanunsu,

Su kuma ji da kunnuwansu,

Su kuma fahimta a zuciyarsu,

Har su juyo gare ni in warkar da su.’

16 Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.

17 Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.

Yesu Ya Ba Da Bayanin Misalin Mai Shuka

18 “To, ga ma’anar misalin mai shukar nan.

19 Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.

20 Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.

21 Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.

22 Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.

23 Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”

Ciyayi a Cikin Alkama

24 Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.

25 Sa’ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.

26 Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.

27 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’

28 Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’

29 Amma ya ce, ‘A’a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.

30 Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”

Misali da Ƙwayar Mastad

31 Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa.

32 Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”

Misali na Yisti

33 Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”

Yesu Ya Yi Amfani da Misalai

34 Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu kome sai da misali.

35 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,

“Zan yi magana da misalai,

Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”

Yesu Ya Ba Da Bayanin Misalin Ciyayi a Cikin Alkama

36 Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”

37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.

38 Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne ‘ya’yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, ‘ya’yan Mugun ne.

39 Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala’iku ne.

40 Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya.

41 Ɗan Mutum zai aiko mala’ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,

42 su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.

43 Sa’an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Dukiyar da Take Binne

44 “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”

Lu’ulu’u Mai Tamanin Gaske

45 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu’ulu’u masu daraja.

46 Da ya sami lu’ulu’u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”

Taru

47 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.

48 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.

49 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala’iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,

50 su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”

Sabuwar Dukiya da Tsohuwa

51 “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”

52 Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”

An Ƙi Yesu a Nazarat

53 Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan.

54 Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami’arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu’ujizan nan?

55 Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? ‘Yan’uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?

56 ‘Yan’uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?”

57 Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”

58 Bai kuma yi mu’ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.