‘Yan Saƙo daga Yahaya Maibaftisma
1 Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa’azi a garuruwansu.
2 To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,
3 su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”
4 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji, da abin da kuka gani.
5 Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.
6 Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”
7 Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?
8 To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.
9 To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa.
10 Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,
‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,
Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’
11 Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.
12 Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi.
13 Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.
14 In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo.
15 Duk mai kunnen ji, yă ji.
16 “To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,
17 ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,
Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba!’
18 “Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da iska.’
19 Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”
Tsawata wa Garuruwan da Ba Su Tuba Ba
20 Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al’ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.
21 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu’ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.
22 Amma ina gaya muku, a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.
23 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A’a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu’ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.
24 Amma ina gaya muku, a Ranar Shari’a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”
Ku Zo Gare Ni, Ku Huta
25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al’amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.
26 Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.
27 Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.
28 Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.
29 Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali’u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.
30 Domin bautata sassauƙa ce, kayana kuma marar nauyi ne.”