Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu
1 Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2 To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan’uwansa Yahaya,
3 da Filibus, da Bartalamawas, da Toma, da Matiyu mai karɓar haraji, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza,
4 da Saminu Bakan’ane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi.
Yesu Ya Aiki Sha Biyu Ɗin
5 Su sha biyun nan ne Yesu ya aika, ya yi musu umarni, ya ce, “Kada ku shiga ƙasar al’ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa.
6 Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama’ar Isra’ila,Irm
7 kuna tafiya, kuna wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’
8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.
9 Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,
10 kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.
11 Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.
12 In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’
13 In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.
14 Kowa kuma ya ƙi yin na’am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.
15 Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari’a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”
Tsanani Mai Zuwa
16 “Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami’arsu.
18 Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al’ummai kuma.
19 A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin.
20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.
21 ‘Dan’uwa zai ba da ɗan’uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. ‘Ya’ya kuma za su tayar wa iyayensu, har su sa a kashe su.
22 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
23 In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
24 “Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba ya fin ubangijinsa.
25 Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba’alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”
Wanda Za a Ji Tsoro
26 “Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.
27 Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.
28 Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.
29 Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba.
30 Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.
31 Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
Bayyana Yarda da Almasihu gaban Mutane
32 “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.
33 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”
Ban Kawo Salama Ba, Sai Takobi
34 “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A’a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
35 Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, ‘ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta.
36 Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa.
37 Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko ‘yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
38 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
39 Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, adana shi yake yi.”
Ayyukan Lada
40 “Wanda ya yi na’am da ku, ya yi na’am da ni ke nan. Wanda ya yi na’am da ni kuwa, to, ya yi na’am da wanda ya aiko ni.
41 Wanda ya yi na’am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na’am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.
42 Kowa ya ba ɗaya daga cikin ‘yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”