ZAK 4

Wahayin Alkuki da Itatuwan Zaitun da Zakariya Ya Gani

1 Mala’ikan da yake Magana da ni ya komo ya farkar da ni kamar yadda akan farkar da mutum daga barci.

2 Sa’an nan ya ce mini, “Me ka gani?”

Sai na ce, “Na ga alkuki wanda aka yi da zinariya tsantsa, da kwano a kansa, da fitilu bakwai a kansa, da butoci bakwai a kan kowace fitilar da yake bisa alkukin.

3 Akwai itatuwan zaitun biyu kusa da alkukin, ɗaya a wajen dama da kwano, ɗaya kuma a wajen hagun.”

4 Sai ni kuma na ce wa mala’ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5 Sa’an nan mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abubuwan nan ba?”

Na ce, “A’a, ubangijina.”

6 Sa’an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.

7 ‘Mene ne kai, ya babban dutse? Za ka zama fili a gaban Zarubabel, zai kuwa kwaso duwatsun da suke ƙwanƙoli da sowa, yana cewa alheri, alheri ne ya kawo haka.’ ”

8 Ubangiji kuma ya yi magana da ni ya ce,

9 “Zarubabel ne ya ɗora harsashin ginin Haikalin nan da hannunsa, shi ne kuma zai gama ginin da hannunsa. Sa’an nan za ka sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni zuwa gare ka.

10 Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”

11 Na ce masa, “Mece ce ma’anar waɗannan itatuwan zaitun da suke wajen dama da hagun alkukin?”

12 Na kuma sāke tambayarsa na ce, “Mece ce ma’anar waɗannan rassan itatuwan zaitun, waɗanda suke kusa da bututu biyu na zinariya, inda mai yake fitowa?”

13 Sai ya ce mini, “Ba ka san ma’anar waɗannan ba?”

Na ce, “A’a, ubangijina.”

14 Sa’an nan ya ce, “Waɗannan su ne keɓaɓɓu biyu waɗanda yake tsaye kusa da Ubangijin dukan duniya.”