HAB 3

Addu’ar Habakuk

1 Addu’ar nasara wadda annabi Habakuk ya yi.

2 Ya Ubangiji, na ji labarinka,

Sai tsoro ya kama ni.

Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu,

Ayyukan da ka saba yi.

Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.

3 Daga Edom Allah ya zo,

Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa.

Ɗaukakarsa ta rufe sammai,

Duniya kuwa ta cika da yabonsa.

4 Walƙiyarsa kamar hasken rana ce,

Haske yana haskakawa daga gare shi,

A nan ne ya lulluɓe ikonsa.

5 Annoba tana tafe a gabansa,

Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.

6 Ya tsaya, ya auna duniya,

Ya duba, sai ya girgiza al’umman duniya.

Sa’an nan madawwaman duwatsu suka farfashe,

Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya.

Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.

7 Na ga alfarwan Kushan suna cikin azaba,

Labulen ƙasar Madayana suna rawar jiki.

8 Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne?

Ko kuwa ka yi fushi da koguna?

Ko kuwa ka hasala da teku ne,

Sa’ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara?

9 Ka ja bakanka,

Ka rantsar da sandunan horo.

Ka rarratsa duniya da koguna.

10 Duwatsu sun gan ka, sun ƙame,

Ruwaye masu hauka suka gudu.

Zurfi kuma ya ta da muryarsa,

Raƙuman ruwansa sun tashi.

11 Rana da wata sun tsaya cik a inda suke,

A lokacin da kibanka masu haske suke wucewa fyu,

Da lokacin walƙatawar hasken māshinka.

12 Ka ratsa duniya da hasala,

Ka kuma tattake al’umman duniya da fushi.

13 Ka fito saboda ceton mutanenka,

Saboda ceton shafaffenka kuma.

Ka fasa kan mugu,

Ka kware shi daga cinya zuwa wuya.

14 Ka kuje kan mayaƙansa da sandunansa,

Waɗanda suka zo kamar guguwa don su watsar da mu.

Suna murna kamar waɗanda suke zaluntar matalauci a ɓoye.

15 Ka tattake teku da dawakanka,

Da haukan ruwa mai ƙarfi.

16 Sa’ad da na ji, sai jikina ya yi rawa,

Leɓunana suka raurawa.

Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki.

Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo

A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.

17 Ko da yake itacen ɓaure bai yi toho ba,

Ba kuma ‘ya’ya a kurangar inabi,

Zaitun kuma bai ba da amfani ba,

Gonaki ba su ba da abinci ba,

An kuma raba garken tumaki daga cikin garke,

Ba kuma shanu a turaku,

18 Duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,

Zan yi murna da Allah Mai Cetona.

19 Ubangiji Allah shi ne ƙarfina,

Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi,

Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.