Ubangiji Ya Amsa wa Habakuk
1 Zan tsaya a wurin tsayawata,
In zauna kuma a kan hasumiya,
In jira in ji abin da zai ce mini,
Da abin da zai amsa a kan kukata.
2 Sai Ubangiji ya ce mini,
“Ka rubuta wahayin da kyau a kan alluna,
Yadda kowa zai karanta shi a sawwaƙe.
3 Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa,
Yana gaggautawa zuwa cikarsa,
Ba zai zama ƙarya ba.
Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri,
Hakika zai zo, ba zai makara ba.
4 Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi,
Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.
5 “Ruwan inabi kuma yana yaudarar mai fariya,
Don haka ba ya zama a gida.
Haɗamarsa tana da fāɗi kamar Lahira,
Kamar kuma mutuwa yake, ba ya ƙoshi.
Ya tattara wa kansa al’ummai duka,
Ya kwaso wa kansa mutane duka.”
Marasa Adalci, Tasu ta Ƙare
6 “Ai, waɗannan duka za su yi ta yi masa zambo,
Su yi masa dariya ta raini,
Su ce, ‘Tasa ta ƙare, shi wanda ya tattara abin da ba nasa ba,
Har yaushe zai riƙa arzuta kansa ta hanyar ba da rance?’
7 Mabartanka za su tasar maka nan da nan,
Waɗanda suke binka bashi za su farka.
Za ka zama ganima a gare su.
8 Saboda ka washe al’umman duniya da yawa,
Sauran mutanen duniya duka za su washe ka,
Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya,
Da birane, da mazauna a cikinsu.
9 “Tasa ta ƙare, shi wanda ya arzuta gidansa da ƙazamar riba,
Ya kuma gina gidansa a bisa don ya tsere wa masifa!
10 Ka jawo wa gidanka kunya,
Saboda ka karkashe mutane da yawa,
Ka hallaka kanka da kanka.
11 Dutse zai yi kuka daga garu,
Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.
12 “Tasa ta ƙare, shi wanda ya gina gari da jini,
Ya kuma kafa birni da mugunta!
13 Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba?
Sun kuma gajiyar da kansu a banza?
14 Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji,
Kamar yadda ruwa ya cika teku.
15 “Taka ta ƙare, kai wanda yake sa maƙwabtanka su sha,
Kana zuba musu dafinka har su bugu,
Don ka dubi tsiraicinsu!
16 A maimakon daraja, za ka sha ƙasƙanci.
Ka sha kai da kanka, ka yi tangaɗi.
Ƙoƙon da yake a hannun Ubangiji zai faɗo a kanka,
Kunya za ta rufe darajarka.
17 Ɓarnar da aka yi wa Lebanon za ta komo kanka,
Ka kashe dabbobinta, yanzu dabbobi za su tsorata ka,
Saboda jinin mutanen da ka zubar,
Da wulakancin da ka yi wa duniya,
Da birane, da mazauna a cikinsu.
18 “Ina amfanin gunki sa’ad da mai yinsa ya siffata shi?
Shi siffa ne da aka yi da ƙarfe, mai koyar da ƙarya.
Gama mai yinsa yakan dogara ga abin da ya siffata,
Sa’ad da ya yi bebayen gumaka.
19 Tasa ta ƙare, shi wanda ya ce da abin da aka yi da itace, ‘Farka!’
Ya kuma ce wa dutse wanda ba ya ji, ‘Tashi!’
Wannan zai iya koyarwa?
Ga shi, an dalaye shi da zinariya da azurfa,
Ba ya numfashi ko kaɗan.
20 “Amma Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,
Bari duniya ta yi tsit a gabansa.”