1 Kaiton birnin jini,
Wanda yake cike da ƙarairayi da
ganima,
Da waso kuma ba iyaka!
2 Ku ji amon bulala da kwaramniyar
ƙafafu,
Da sukuwar doki da girgizar karusai!
3 Sojojin dawakai suna kai sura,
Takuba suna walƙiya, māsu suna
ƙyalƙyali.
Ga ɗumbun kisassu, da tsibin
gawawwaki,
Matattu ba su ƙidayuwa,
Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!
4 Ya faru saboda yawan karuwancin
Nineba kyakkyawa mai daɗin
baki,
Wadda ta ɓad da al’umman duniya
da karuwancinta,
Ta kuma ɓad da mutane da daɗin
bakinta.
5 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ina
gāba da ke,
Zan kware fatarinki a idonki,
Zan sa al’ummai da mulkoki su dubi
tsiraicinki.
6 Zan watsa miki ƙazanta,
In yi miki wulakanci,
In maishe ki abin raini.
7 Dukan waɗanda za su dube ki
Za su ja da baya su ce,
‘Nineba ta lalace, wa zai yi kuka
dominta?’
A ina zan samo miki waɗanda za su
ta’azantar da ke?”
8 Kin fi No ne?
Wadda take a bakin Nilu,
Wadda ruwa ya kewaye ta?
Teku ce kagararta.
Ruwa ne kuma garunta.
9 Habasha da Masar su ne ƙarfinta
marar iyaka,
Fut da Libiya su ne kuma
mataimakanta.
10 Duk da haka an tafi da ita, an kai ta
cikin bauta.
An fyaɗa ƙanananta a ƙasa,
An yi kacakaca da su a kowace
mararraba.
An jefa kuri’a a kan manyan
mutanenta,
Aka ɗaure dukan manyan mutanenta
da sarƙoƙi.
11 Ke Nineba kuma za ki bugu,
Za a ɓoye ki.
Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.
12 Dukan kagaranki suna kama da
itatuwan ɓaure,
Waɗanda ‘ya’yansu suka harba.
Da an girgiza sai su faɗo a bakin mai
sha.
13 Sojojinki kamar mata suke a
tsakiyarki!
An buɗe wa maƙiyanki ƙofofin
ƙasarki.
Wuta za ta cinye madogaran
ƙofofinki.
14 Ki tanada ruwa domin za a kewaye
ki da yaƙi!
Ki ƙara ƙarfin kagaranki!
Ki tafi kududdufi, ki kwaɓa laka!
Ki ɗauki abin yin tubali!
15 A can wuta za ta cinye ki,
Takobi zai sare ki,
Zai cinye ki kamar fara.
Ki riɓaɓɓanya kamar fara.
Ki kuma riɓaɓɓanya kamar ɗango.
16 Kin yawaita ‘yan kasuwanki suna da
yawa fiye da taurari,
Amma sun tafi kamar fara waɗanda
sukan buɗe fikafikansu su tashi, su
tafi.
17 Shugabanninki kamar ɗango suke,
Manyan mutanenki kamar
cincirindon fāra ne,
Suna zaune a kan shinge a kwanakin
sanyi,
Sa’ad da rana ta fito, sukan tashi su
tafi,
Ba wanda ya san inda suke.
18 Ya Sarkin Assuriya, masu tsaronka
suna barci,
Manyan mutanenka suna
kwankwance,
Mutanenka sun watse cikin
duwatsu,
Ba wanda zai tattaro su.
19 Ba abin da zai rage zafin rauninka,
Rauninka ba ya warkuwa.
Duk wanda ya ji labarinka, zai tafa
hannuwansa
Gama wane ne ba ka musguna wa
ba?