NAH 2

1 Wanda yake farfashewa ya auko

maka,

Sai ka sa mutane a kagara, a yi

tsaron hanya,

Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinka

duka.

2 Gama Ubangiji zai mayar wa

Yakubu da darajarsa kamar ta

Isra’ila.

Ko da masu washewa sun washe su,

Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.

3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne,

Sojojinsa kuma suna saye da mulufi.

Da ya shirya tafiya,

Karusai suna walƙiya kamar

harshen wuta,

Ana kaɗa mashi da bantsoro.

4 Karusai sun zabura a tituna a

haukace.

Suna kai da kawowa a dandali,

Suna walwal kamar jiniya,

Suna sheƙawa a guje kamar

walƙiya.

5 Sai aka kira shugabanni,

Suka zo a guje suna tuntuɓe,

Suka gaggauta zuwa garu,

Suka kafa kagara.

6 An buɗe ƙofofin kogi,

Fāda ta rikice.

7 An tsiraita sarauniya, an tafi da ita,

‘Yan matanta suna makoki, suna

kuka kamar kurciyoyi,

Suna bugun ƙirjinsu.

8 Nineba tana kama da tafki wanda

ruwansa yake zurarewa,

Suna cewa, “Tsaya, tsaya,”

Amma ba wanda ya waiga.

9 A washe azurfa!

A washe zinariya!

Dukiyar ba ta da adadi,

Akwai dukiya ta kowane iri.

10 Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama

kufai!

Zukata sun narke, gwiwoyi suna

kaɗuwa!

Kwankwaso yana ciwo,

Fuskoki duka sun kwantsare!

11 Ina kogon nan na zakoki,

Inda aka ciyar da ‘ya’yan zaki,

Inda zaki da zakanya da

kwiyakwiyansu sukan tafi,

Su tsere daga fitina?

12 Zaki ya kashe abin da ya ishi

kwiyakwiyansa.

Ya kaso wa zakanyarsa abin da ya

ishe ta.

Ya cika kogonsa da ganima.

Ragargajewar Nineba

13 “Ga shi, ina gāba da ke. Ni Ubangiji

Allah Mai Runduna na faɗa.

Zan ƙone karusanki,

Takobi kuwa zai karkashe sagarun

zakokinki,

Zan hana miki ganima a duniya.

Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunki

ba.”