Fushin Ubangiji a kan Nineba
1 Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.
2 Ubangiji Allah mai kishi ne, mai
sakayya,
Ubangiji mai sakayya ne, mai
hasala.
Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan
maƙiyansa.
Yana tanada wa maƙiyansa fushi.
3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne,
Mai Iko Dukka.
Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi
ba.
Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin
hadiri,
Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.
4 Yakan tsauta wa teku, sai teku ta
ƙafe.
Yakan busar da koguna duka.
Bashan da Karmel sukan bushe,
Tohon Lebanon yakan yanƙwane.
5 Duwatsu sukan girgiza a gabansa,
Tuddai kuma su narke.
Duniya ta murtsuke a gabansa,
Da dukan mazauna a cikinta.
6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa?
Wa kuma zai iya daurewa da
hasalarsa?
Yana zuba hasalarsa mai kama da
wuta,
Duwatsu sukan farfasu a gabansa.
7 Ubangiji mai alheri ne,
Shi mafaka ne a ranar wahala.
Ya san waɗanda suke fakewa a gare
shi.
8 Zai shafe maƙiyansa da ambaliyar
ruwa,
Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwa
cikin duhu.
9 Me kuke ƙullawa game da Ubangiji?
Ubangiji zai wofintar da abin nan da
kuke ƙullawa,
Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.
10 Suna maye da abin shansu,
Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya,
Da busasshiyar ciyawa.
11 Daga cikinki wani ya fito,
Wanda ya ƙulla wa Ubangiji
makirci,
Ya ƙulla shawara marar amfani.
12 Ni Ubangiji na ce,
“Ko da yake suna da ƙarfi, suna
kuma da yawa,
Za a datse su, su ƙare.
Ko da yake na wahalar da kai,
Ba zan ƙara wahalar da kai ba.
13 Yanzu zan karya karkiyarsa daga
wuyanka,
Zan kuma tsinke sarƙarta.”
14 Ubangiji ya riga ya yi umarni a
kanka cewa,
“Sunanka ba zai ci gaba ba,
Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi
Da siffofi na zubi daga gidan
gumakanka.
Zan shirya maka kabari, gama kai
rainanne ne.”
Labarin Fāɗuwar Nineba
15 Duba a kan duwatsu, ƙafafun
wanda yake kawo albishir,
Wanda yake shelar salama!
Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka,
Ka kuma cika wa’adodinka.
Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yi
gāba da kai ba,
An datse shi ƙaƙaf.