MIKA 6

Ubangiji Yana Gāba da Isra’ila

1 “Ku ji abin da ni Ubangiji

nake cewa,

Tashi ku gabatar da ƙararku a

gaban duwatsu,

Ku bar tuddai su ji muryarku.

2 “Ku duwatsu da madawwaman tussan

duniya,

Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi

muku.

Gama Ubangiji, yana da magana

gāba da mutanensa,

Zai tuhumi Isra’ila.

3 “Ya ku jama’ata, me na yi muku?

Wace irin fitina nake yi muku?

Ku amsa mini!

4 Gama na fito da ku daga ƙasar

Masar,

Na fanshe ku daga gidan bauta.

Na aika muku da Musa, da Haruna,

da Maryamu.

5 Ya ku jama’ata, ku tuna

Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya

ƙulla,

Da yadda Bal’amu ɗan Beyor ya

amsa masa,

Da abin da ya faru daga Shittim, har

zuwa Gilgal,

Don ku san ayyukan adalci na

Ubangiji.”

Abin da Allah Yake So ga Mutane

6 Da me zan zo gaban Ubangiji,

In sunkuyar da kaina a gaban Allah

na Sama?

Ko in zo gabansa da maraƙi bana

ɗaya domin yin hadaya ta

ƙonawa?

7 Ubangiji zai yi murna da raguna

dubbai

Ko kuwa da kogunan mai dubbai?

Zan ba da ɗan farina ne don

laifina?

Ko kuwa zan ba da ‘ya’yana saboda

zunubina?

8 Ya kai mutum, ya riga ya nuna

maka abin da yake mai kyau.

Abin da Ubangiji yake so gare ka,

shi ne

Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata

alheri,

Ka bi Allah da tawali’u.

9 Ubangiji yana kira ga birnin.

Hikima ce ƙwarai a ji tsoron

sunanka.

“Ki ji ya kabila, wa ya sa miki

lokacinki?

10 Ba zan manta da dukiya ta mugunta

a gidan mugu ba,

Ba kuwa zan manta da bugaggen

mudun awo ba.

11 Zan kuɓutar da mutum mai ma’auni

na cuta

Da ma’aunin ƙarya?

12 Attajiran birnin sun cika zalunci,

Mazaunansa kuwa maƙaryata ne,

Harshensu na yaudara ne.

13 Domin haka zan buge ku da ciwo,

In maishe ku kufai saboda

zunubanka.

14 Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba,

Yunwa za ta kasance a cikinku,

Za ku tanada, amma ba zai tanadu

ba,

Abin da kuma kuka tanada zan bai

wa takobi.

15 Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba.

Za ku matse ‘ya’yan zaitun, amma

ba za ku shafa mansa ba,

Za ku kuma matse ‘ya’yan inabi,

amma ba za ku sha ruwansa ba.

16 Domin kun kiyaye dokokin Omri,

Kun bi halin gidan Ahab,

Kun kuma bi shawarwarinsu.

Domin haka zan maishe ku kufai,

In mai da ku abin dariya,

Za ku sha raini a wurin mutanena.”