AMOS 8

Wahayi na Huɗu, Kwandon Ɓaure na Ci

1 Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.

2 Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?”

Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.”

Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama’ata Isra’ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.

3 Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko’ina. Ba za a ji motsin kome ba.”

An kai Ƙarshen Isra’ila

4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.

5 Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa

keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce,

Mu sami damar yin kasuwancinmu.

Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne?

Ko mā sami damar kai hatsinmu

kasuwa,

Mu sayar musu da tsada,

Mu yi awo da ma’aunin zalunci,

Mu daidaita ma’auni yadda za mu

cuci mai saya?

6 Za mu sayi matalauci da azurfa ya

zama bawa,

Mai fatara kuma da takalma

bi-shanu.

Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi,

Mu ci riba mai yawa.”

7 Ubangiji Allahn Isra’ila ya riga ya

rantse,

Ya ce, “Ba zan manta da mugayen

ayyukanku ba.

8 Shi ya sa ƙasar za ta girgiza,

Duk wanda yake cikinta zai yi baƙin

ciki.

Ƙasa duka za ta girgiza.

Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.

9 A wannan lokaci rana za ta fāɗi da

tsakar rana,

Duniya ta duhunta da rana kata.

Ni, Ubangiji ne na faɗa.

10 Zan mai da bukukuwanku makoki,

In sa waƙoƙinku na murna su zama

na makoki.

Zan sa muku tufafin makoki,

In sa ku aske kanku.

Za ku yi makoki kamar iyayen da

suka rasa tilon ɗansu.

Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.

11 “Lokaci yana zuwa da zan aiko da

yunwa a ƙasar.

Mutane za su ji yunwa,

Ba ta abinci ba,

Za su ji ƙishi,

Ba na ruwa ba.

Za su ji yunwar rashin samun saƙo

daga wurin Ubangiji.

Ni Ubangiji ne, na faɗa.

12 Mutane za su raunana, su riƙa kai

da kawowa,

Daga gabas zuwa yamma, daga

kuma kudu zuwa arewa.

Za su dudduba ko’ina suna neman

saƙo daga Ubangiji,

Ba kuwa za su samu ba.

13 A ranan nan kyawawan ‘yan mata

da samari

Za su faɗi saboda ƙishirwa.

14 Waɗanda suka yi rantsuwa da

gumakan Samariya,

Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da

gunkin Dan,

Da ran gunkin Biyer-sheba,’

Irin waɗannan mutane za su fāɗi,

Ba za su ƙara tashi ba.”