Halakar Isra’ila
1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman
sakewa a Sihiyona,
Da ku da kuke tsammani kuna
zaman lafiya a Samariya,
Ku da kuke manyan mutane
Na wannan babbar al’umma ta
Isra’ila,
Waɗanda jama’a suke zuwa a gare su
neman taimako!
2 Ku je ku duba a birnin Kalne.
Sa’an nan ku zarce zuwa babban
birnin Hamat,
Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.
Sun fi mulkin Yahuza da Isra’ila ne?
Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi
naku?
3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan
rana ta masifa,
Amma ga shi, goyon bayan hargitsi
kuke ta yi,
Ta wurin ayyukanku.
4 Taku ta ƙare, ku da kuke kwance
kan gadajen hauren giwa,
Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayen
kujerunku,
Ku ci naman maraƙi da na rago.
5 Kukan so ku tsara waƙoƙi kamar
yadda Dawuda ya yi,
Ku raira su da garayu.
6 Da manyan kwanoni kuke shan
ruwan inabi,
Ku shafe jiki da mai mafi kyau,
Amma ba ku yin makoki saboda
lalacewar Isra’ila.
7 Don haka, ku ne na fari da za a sa su
yi ƙaura
Bukukuwanku da shagulgulanku za
su ƙare.
8 Ubangiji kansa ne ya rantse.
Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,
“Ba na son girmankai na jama’ar
Isra’ila.
Ba na son fādodinsu.
Zan ba da birnin da dukan abin da
yake cikinsa ga abokan gābansu.”
9 Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.
10 Sa’ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”
Sai a amsa, “A’a.”
Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”
11 Sa’ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.
12 Dawakai sukan yi sukuwa a
duwatsu?
Ana huɗan teku da garmar
shanu?
Duk da haka kuka mai da adalci
dafi,
Kuka mai da nagarta, mugunta.
13 Kuna fariyar cin garin Lodebar, wato
wofi, da yaƙi.
Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ci
Karnayim, wato ƙaho biyu, da
yaƙi.”
14 Ubangiji Allah Mai Runduna
kansa, ya amsa ya ce,
“Zan aiko da wata al’umma ta yi
gāba da ku, ya Isra’ilawa.
Za ta matse muku
Tun daga mashigin Hamat wajen
arewa,
Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”