Mowab
1 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Mowab sun ci gaba da
yin zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun ƙone ƙasusuwan Sarkin
Edom
Don su yi toka da su.
2 Zan aukar da wuta a ƙasar
Mowab,
Ta ƙone kagarar Keriyot.
Jama’ar Mowab za su mutu a
hargitsin yaƙi,
Sa’ad da sojoji suke sowa, ana busa
ƙahoni.
3 Zan kashe Sarkin Mowab da
shugabannin ƙasar.”
Yahuza
4 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Yahuza sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun raina koyarwata sun ƙi
bin umarnaina.
Allolinsu na ƙarya waɗanda
kakanninsu suka bauta wa,
Sun sa su su ratse daga hanya.
5 Saboda haka zan aukar da wuta a
kan Yahuza
Ta ƙone kagarar Urushalima.”
Allah Ya Hukunta Isra’ila
6 Ubangiji ya ce,
“Mutanen Isra’ila sun ci gaba da yin
zunubi.
Hakika, zan hukunta su,
Don sun sayar da salihai waɗanda
suka kāsa biyan bashinsu.
Sun kuma sayar da matalauta
Waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin
bi-shanu ba.
7 Sun tattake marasa ƙarfi da
kāsassu,
Suna tunkuɗe matalauta su wuce.
Tsofaffi da samari sukan tafi wurin
karuwan Haikali.
Ta haka suke ɓata sunana mai
tsarki.
8 A duk wuraren sujadarsu sukan
kwanta
A bisa tufafin da suka karɓe jingina.
A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha
ruwan inabi
Da suka karɓo daga wurin waɗanda
suke bi bashi.
9 “Amma ga shi, saboda ku na
hallakar da Amoriyawa,
Dogayen mutanen nan masu kama
da itatuwan al’ul,
Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak,
Na hallaka su ƙaƙaf.
10 Na fito da ku, wato jama’ata daga
Masar.
Na bi da ku cikin jeji shekara
arba’in,
Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa ta
zama taku.
11 Na zaɓi waɗansu daga cikin
‘ya’yanku su zama annabawa,
Waɗansu kuma daga cikin samarinku
su zama keɓaɓɓu.
Ko ba haka ba ne, ya ku
Isra’ilawa?
Ni, Ubangiji, na yi magana.
12 Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwan
inabi,
Kuka kuma umarci annabawa kada
su isar da saƙona.
13 Zan danƙare ku a inda kuke
Kamar yadda ake danƙare
amalanke da kayan tsaba.
14 Ko masu saurin gudu ma ba za su
tsere ba,
Ƙarfafa za su zama kumamai,
Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu
ba.
15 ‘Yan baka ba za su iya ɗagewa ba.
Masu saurin gudu ba za su tsira ba.
Mahayan dawakai kuma ba za su
tsere da rayukansu ba.
16 Ko sojojin da suka fi jaruntaka duka
ma,
Za su gudu tsirara a ran nan.”
Ubangiji ne ya faɗa.