Shari’ar Al’ummai
1 “A wannan lokaci zan mayar wa
Yahuza da Urushalima da
wadatarsu.
2 Zan tattara dukan al’ummai,
In kai su kwarin Yehoshafat.
A can zan yi musu shari’a
A kan dukan abin da suka yi wa
jama’ata.
Sun warwatsa Isra’ilawa a sauran
ƙasashe,
Suka rarraba ƙasata.
3 Sun jefa kuri’a a kan mutanena,
Sun sayar da yara, mata da maza,
zuwa bauta
Don su biya karuwai da ruwan
inabi.
4 “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.
5 Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.
6 Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa’an nan kun sayar da su ga Helenawa.
7 Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.
8 Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza ‘ya’yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”
9 Ku sanar wa al’ummai da wannan,
Su yi shirin yaƙi,
Su kira mayaƙa!
Su tattaro sojoji, su zo!
10 Su bubbuge allunan garmunansu,
Su yi takuba da su.
Su ƙera māsu da wuƙaƙen da ake
yi wa itatuwa aski.
Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumi
ne!”
11 Su gaggauta, su zo su al’ummai da
suke kewaye,
Su tattaru a kwarin.
“Ya Ubangiji, ka saukar da
rundunarka mai ƙarfi.”
12 “Sai al’ummai su yi shiri,
Su zo kwarin Yehoshafat,
Gama a can zan zauna in shara’anta
al’umman da suke kewaye,
13 Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi.
Su shiga su tattaka,
Gama wurin matsewar ruwan inabi
ya cika.
Manyan randuna sun cika suna
tumbatsa,
Gama muguntarsu da yawa take.”
14 Dubun dubbai suna cikin kwarin da
za a yanke shari’a!
Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa a
kwarin yanke shari’a.
15 Rana da wata sun yi duhu,
Taurari kuma ba su haskakawa.
Ceton Yahuza
16 Ubangiji yana magana da ƙarfi daga
Sihiyona,
Yana tsawa daga Urushalima,
Sammai da duniya sun girgiza.
Amma Ubangiji shi ne mafakar
jama’arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra’ila.
17 “Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji
Allahnku,
Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna
tsattsarka.
Urushalima kuma za ta tsarkaka,
Sojojin abokan gāba ba za su ƙara
ratsawa ta cikinta ba.
18 “A wannan lokaci tsaunuka za su rufu
da kurangar inabi,
Tuddai za su cika da shanu,
Dukan rafuffukan Yahuza za su
gudano da ruwa,
Maɓuɓɓuga za ta gudano daga
Haikalin Ubangiji,
Ta shayar da kwarin Shittim.
19 “Masar za ta zama hamada,
Edom kuma za ta zama kufai,
Saboda kama-karya da suka yi wa
mutanen Yahuza,
Saboda sun zubar da jinin marasa
laifi a ƙasarsu,
20 Za a zauna a Yahuza da Urushalima
dukan tsararraki har abada.
21 Zan sāka alhakin jininsu,
Ba zan kuɓutar da mai laifi ba,
Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”
Sihiyona.”