Ɓarnar Fāra
1 Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.
2 Ku dattawa, ku kasa kunne,
Bari kowa da kowa da yake cikin
Yahuza, ya kasa kunne.
Wani abu mai kamar wannan ya taɓa
faruwa a lokacinku,
Ko a lokacin kakanninku?
3 Ku faɗa wa ‘ya’yanku labarinsa,
‘Ya’yanku kuma su faɗa wa
‘ya’yansu,
‘Ya’yansu kuma su faɗa wa tsara
mai zuwa.
4 Abin da ɗango ya bari fara ta ci,
Abin da fara ta bari burduduwa ta
ci.
5 Ku farka, ku yi ta kuka, ku
bugaggu,
Ku yi kuka, ku mashayan ruwan
inabi,
An lalatar da ‘ya’yan inabin
Da ake yin sabon ruwan inabi da su.
6 Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,
Tana da ƙarfi, ba ta kuma
ƙidayuwa,
Haƙoranta suna da kaifi kamar na
zaki.
7 Ta lalatar da kurangar inabinmu,
Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.
Ta gaigaye ɓawo duka,
Saboda haka rassan sun zama fari
fat.
8 Ya jama’a, ku yi kuka
Kamar yarinyar da take makokin
rasuwar saurayinta.
9 Ba hatsi ko ruwan inabin
Da za a yi hadaya da su cikin
Haikalin.
Firistoci masu miƙa wa Ubangiji
hadaya suna makoki.
10 Ba kome a gonaki,
Ƙasa tana makoki,
Domin an lalatar da hatsin,
‘Ya’yan inabi sun bushe,
Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.
11 Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,
Ku yi kuka, ku da kuke lura da
gonakin inabi,
Gama alkama, da sha’ir,
Da dukan amfanin gonaki sun
lalace.
12 Kurangar inabi ta bushe,
Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,
Rumman, da dabino, da gawasa,
Da dukan itatuwan gonaki sun
bushe.
Murna ta ƙare a wurin mutane.
13 Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a
bagaden Ubangiji,
Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka!
Ku shiga Haikali, ku kwana,
Kuna saye da tufafin makoki,
Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za
a yi hadaya da su,
A cikin Haikalin Allahnku.
14 Ku sa a yi azumi,
Ku kira muhimmin taro.
Ku tara dattawa da dukan mutanen
ƙasar
A Haikalin Ubangiji Allahnku,
Ku yi kuka ga Ubangiji.
15 Taku ta ƙare a wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.
16 An lalatar da amfanin gonaki a kan
idonmu,
Ba murna a Haikalin Allahnmu.
17 Itatuwa sun mutu a busasshiyar
ƙasa,
Ba hatsin da za a adana a rumbu,
Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.
18 Dabbobi suna nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
Domin ba su da makiyaya.
Garkunan tumaki da awaki kuma
suna shan azaba.
19 Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji,
Domin ciyayi da itatuwa sun bushe,
Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.
20 Har ma namomin jeji suna kuka a
gare ka,
Domin rafuffuka sun bushe,
Ciyayi kuma sun bushe,
Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.