1 Ifraimu tana kiwon iska,
Tana ta bin iskar gabas dukan yini.
Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya.
Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya,
Tana kai mai a Masar.”
2 Ubangiji yana da magana game da mutanen Yahuza,
Zai hukunta Isra’ila saboda hanyoyinta,
Zai sāka mata gwargwadon ayyukanta.
3 A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan’uwansa,
Sa’ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.
4 Ya yi kokawa da mala’ika ya yi rinjaye.
Ya yi kuka, ya roƙi albarka.
Ya sadu da Allah a Betel,
A can Allah ya yi magana da shi.
5 Ubangiji Allah Mai Runduna,
Sunansa Ubangiji,
6 Sai ku koma wurin Allahnku,
Ku yi alheri, ku yi adalci,
Ku saurari Allahnku kullayaumin.
7 Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma’aunin algus a hannunsa.
Yana jin daɗin yin zalunci.
8 Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai,
Mun samar wa kanmu dukiya.
A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’
9 Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar,
Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai,
Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.
10 “Na yi magana da annabawa,
Ni ne na ba da wahayi da yawa,
Da misalai kuma ta wurin annabawa.
11 Idan akwai laifi a Gileyad,
Hakika za su zama wofi.
A Gilgal ana sadaka da bijimai,
Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsu
A gyaffan kunyoyin gona.”
12 Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram,
A can Isra’ila ya yi barantaka saboda mace,
Saboda mace ya yi kiwon tumaki.
13 Ta wurin annabi Ubangiji ya fito da mutanen Isra’ila daga Masar,
Ta wurin annabi kuma ya kiyaye su.
14 Mutanen Ifraimu sun yi muguwar tsokana mai ta da fushi,
Domin haka Ubangiji zai ɗora musu hakkin jini a kansu,
Zai saka musu cin mutuncin da suka yi.