Rubutu a Bango
1 Sarki Belshazzar ya yi wa dubban manyan mutanensa liyafa, ya kuwa sha ruwan inabi a gabansu.
2 Da Belshazzar ya kurɓa ruwan inabin, sai ya umarta a kawo tasoshi na zinariya da na azurfa waɗanda Nebukadnezzar ubansa ya kwaso daga Haikali a Urushalima, domin sarki, da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa su sha ruwan inabi da su.
3 Sai suka kawo tasoshin zinariya da na azurfa waɗanda aka kwaso daga cikin Haikali, wato Haikalin Allah a Urushalima. Sai sarki da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa, suka yi ta sha da su.
4 Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.
5 Nan da nan sai yatsotsin hannun mutum suka bayyana, suka yi rubutu a kan shafen bangon fādar sarkin, wanda yake daura da fitila. Sarki kuwa yana ganin hannun sa’ad da hannun yake rubutu.
6 Sai fuskar sarki ta turɓune, tunaninsa suka razanar da shi, gaɓoɓinsa suka saki, gwiwoyinsa suka soma bugun juna.
7 Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma’anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”
8 Sai dukan masu hikima na sarki suka shigo, amma ba wanda ya iya karanta rubutun balle ya faɗa wa sarki ma’anarsa.
9 Belshazzar sarki fa ya firgita ƙwarai, fuskarsa ta turɓune, fādawansa duk suka ruɗe.
10 Da sarauniya ta ji maganganun sarki da na manyan fādawansa, sai ta shiga babban ɗakin da ake liyafar, ta ce, “Ran sarki, ya daɗe! Kada ka firgita, kada kuma fuskarka ta turɓune.
11 Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.
12 Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar ka-cici-ka-cici, da warware al’amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma’anar.”
Daniyel ya Karanta Rubutun ya kuma Faɗi Ma’anarsa
13 Sai aka kawo Daniyel a gaban sarki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda ubana ya kawo daga Yahuza?
14 Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima.
15 Yanzun nan aka kawo mini masu hikima, da masu dabo don su karanta wannan rubutu, su kuma bayyana mini ma’anarsa, amma sun kāsa faɗar ma’anar rubutun.
16 Amma na ji ka iya fassara, ka kuma iya warware al’amura masu wuya. Idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya bayyana mini ma’anarsa, to, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin mulkin ƙasar.”
17 Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma’anarsa.
18 “Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.
19 Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.
20 Amma sa’ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
21 Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar ‘yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
22 “Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.
23 Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
24 “Domin haka Allah ya aiko da wannan hannu da ya yi rubutun nan.
25 Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN.
26 Ma’anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare.
27 Ma’anar TEKEL ita ce an auna ka a ma’auni, aka tarar ka kāsa.
28 Ma’anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”
29 Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.
30 A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.
31 Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.