Addu’ar Ezra da Faɗar Laifi
1 Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra’ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa.
2 Gama sun auro wa kansu da ‘ya’yansu ‘yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”
3 Sa’ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.
4 Sa’an nan dukan waɗanda suka yi rawar jiki saboda maganar Allah na Isra’ila, saboda rashin aminci na waɗanda suka komo daga zaman talala, suka taru, suka kewaye ni sa’ad da nake zaune a ruɗe, har lokacin yin sadakar yamma.
5 A lokacin sadakar yamma ɗin, sai na tashi daga yin azumi, da rigata da alkyabbata yagaggu. Na rusuna a gwiwoyina, na ɗaga hannuwana zuwa ga Ubangiji Allahna.
6 Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.
7 Tun daga zamanin kakanninmu muna da babban laifi. Saboda zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu, aka bashe mu a hannun sarakunan waɗansu ƙasashe, aka bashe mu ga takobi, aka kai mu bauta, aka washe mu, aka kunyatar da mu kamar yadda yake a yau.
8 Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana alheri da ya bar mana ringi, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, inda za mu zauna lafiya domin Allahnmu ya waye mana ido, ya kuma ba mu ‘yar wartsakewa daga bautarmu.
9 Gama mu bayi ne, duk da haka Allahnmu bai manta da mu a bautarmu ba, amma ya sa muka sami tagomashi a wurin sarakunan Farisa, suka iza mu domin mu gina Haikalin Allahnmu, mu sāke gyaransa, mu kuma gina garu a Yahuza da Urushalima.
10 “Yanzu, me za mu ce bayan wannan, ya Allahnmu, gama mun manta da umarnanka.
11 Umarnan da ka umarta ta bakin bayinka annabawa cewa, ‘Ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta, ta ƙazantu da ƙazantar al’umman da take cikinta. Ƙazantarsu ta cika dukan ƙasar.
12 Domin haka kada ku aurar musu da ‘ya’yanku mata, kada kuma ku auro wa ‘ya’yanku ‘yan matansu, kada kuma ku nemi zaman arziki da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku ci albarkar ƙasar, har ku bar ta gādo ga ‘ya’yanku har abada.’
13 Bayan wannan dukan abubuwan nan suka same mu saboda mugayen ayyukanmu da zunubanmu masu yawa. Ya Allahnmu, ga shi ma, ka hukunta mu kaɗan bisa ga yawan zunubanmu, ka kuma bar mana wannan ringi.
14 Za mu sake ƙetare umarninka, mu yi aurayya da mutanen da suke yin waɗannan ƙazanta? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ringi ba?
15 Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne, gama ka bar mana ringin da ya tsira kamar yadda yake a yau. Ga mu nan gabanka da zunubinmu, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka saboda wannan.”