EZRA 8

Waɗanda Suka Komo daga Zaman Talala

1 Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. Wannan kuwa shi ne lissafin asalin waɗanda suka komo tare da ni daga Babila a zamanin sarautar sarki Artashate.

2-14 Gershom shi ne shugaban iyalin Finehas,

Daniyel shi ne na iyalin Itamar,

Hattush ɗan Shekaniya, shi ne na iyalin Dawuda.

Zakariya shi ne na iyalin Farosh, ya zo da iyalinsa mutum ɗari da hamsin.

Eliyehoyenai ɗan Zarahiya, shi ne na iyalin Fahat-mowab, tare da shi kuma akwai mutum ɗari biyu.

Shekaniya ɗan Yahaziyel, shi ne na iyalin Zattu, tare da shi akwai mutum ɗari uku.

Ebed ɗan Jonatan, shi ne na iyalin Adin, tare da shi akwai mutum hamsin.

Yeshaya ɗan Ataliya, shi ne na iyalin Elam, yana tare da mutum saba’in.

Zabadiya ɗan Maikel, shi ne na iyalin Shefatiya, yana tare da mutum tamanin.

Obadiya ɗan Yehiyel, shi ne na iyalin Yowab, yana tare da mutum ɗari biyu da goma sha takwas.

Shelomit ɗan Yosifiya, shi ne na iyalin Bani, yana tare da mutum ɗari da sittin.

Zakariya ɗan Bebai, shi ne na iyalin Bebai, yana tare da mutum ashirin da takwas.

Yohenan ɗan Hakkatan, shi ne na iyalin Azgad, yana tare da mutum ɗari da goma.

Elifelet, da Yehiyel, da Shemaiya, su ne na iyalin Adonikam (su ne suka zo daga baya), suna tare da mutum sittin.

Utai da Zabbud, su ne na iyalin Bigwai, suna tare da mutum saba’in.

Ezra Ya Sami Lawiyawa domin Haikali

15 Na kuma tara mutanen a bakin rafin da yake gudu zuwa Ahawa. A nan muka yi zango kwana uku. Sa’ad da na duba jama’a, da firistoci, sai na tarar ba ‘ya’yan Lawi.

16 Sai na sa a kirawo Eliyezer, da Ariyel, da Shemaiya, da Elnatan, da Yarib, da Elnatan, da Natan, da Zakariya, da Mehullam waɗanda suke shugabanni, a kuma kirawo Yoyarib da Elnatan masu hikima.

17 Na kuma aike su zuwa wurin Iddo, shugaba a Kasifiya. Na faɗa musu abin da za su faɗa wa Iddo a Kasifiya da ‘yan’uwansa ma’aikatan Haikali, wato ya aiko mana waɗanda za su yi hidima a Haikalin Allahnmu.

18 Da yake Allah yana tare da mu, sai suka kawo mana mutum mai ganewa daga ‘ya’yan Mali ɗan Lawi, ɗan Isra’ila. Sunan mutumin Sherebiya, da ‘ya’yansa da ‘yan’uwansa, su goma sha takwas ne.

19 Suka kuma kawo Hashabiya tare da Yeshaya daga ‘ya’yan Merari. ‘Yan’uwansa da ‘ya’yansu su ashirin ne.

20 Da kuma ma’aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma’aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.

Ezra Ya Bi da Jama’a da Azumi da Addu’a

21 Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da ‘ya’yanmu, da kayanmu a hanya.

22 Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”

23 Don haka muka yi azumi, muka roƙi Allah saboda wannan, shi kuwa ya ji roƙonmu.

Kyautai domin Haikalin

24 Sai na keɓe goma sha biyu daga cikin manyan firistoci, wato Sherebiya, da Hashabiya, da waɗansu goma daga cikin danginsu.

25 Na auna musu azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda sarki da fādawansa, da manyan mutanensa, da Isra’ilawa duka suka kawo suka miƙa domin Haikalin Allahnmu.

26-27 Ga abin da na auna na ba su,

talanti ɗari shida da hamsin na azurfa

kayan azurfa na talanti ɗari

kayan zinariya na talanti ɗari

kwanonin zinariya guda ashirin na darik dubu (1,000)

kwanoni guda biyu na tatacciyar tagulla, darajarsu daidai da kwanon zinariya.

28 Na ce musu, “Ku tsarkaka ne ga Ubangiji, kayayyakin kuma tsarkaka ne, azurfa da zinariya sadaka ce ta yardar rai ga Ubangiji Allah na kakanninku.

29 Ku riƙe su, ku yi tsaronsu, har lokacin da za ku kai su a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanninku na Isra’ila a Urushalima, a shirayin Haikalin Ubangiji.”

30 Sai firistoci da Lawiyawa suka ɗauki azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda aka auna, zuwa Urushalima, zuwa Haikalin Allahnmu.

Komowar Urushalima

31 Muka kuwa tashi daga kogin Ahawa a ran goma sha biyu ga watan ɗaya, don mu tafi Urushalima, Allahnmu kuma yana tare da mu, ya kuwa cece mu daga hannun maƙiyanmu, da mafasa a hanya.

32 Muka iso Urushalima, muka yi kwana uku.

33 A rana ta huɗu, a Haikalin Allah, sai aka ba da azurfa, da zinariya, da kwanoni ga Meremot ɗan Uriya, firist, da Ele’azara ɗan Finehas, da Lawiyawa, wato Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.

34 Aka ƙidaya dukan kome aka kuma auna, sa’an nan aka rubuta yawan nauyin.

35 Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra’ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra’ila,da raguna tasa’in da shida, da ‘yan raguna saba’in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

36 Suka faɗa wa wakilan sarki da masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis umarnan sarki. Su kuwa suka taimaki mutane, da kuma Haikalin Allah.