Alkawarin Zuwan Ubangiji
1 Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakar da sahihan zukatanku ta hanyar tuni.
2 Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.
3 Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna biye wa muguwar sha’awarsu,
4 suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”
5 Da gangan suke goce wa maganar nan, cewa tun dā dā ta wurin maganar Allah sammai suka kasance, aka kuma siffata ƙasa daga ruwa, tana kuma a tsakiyar ruwa.
6 Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.
7 Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari’a, a hallaka su.
8 Amma ya ku ƙaunatattuna kada ku goce wa magana gudar nan, cewa ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekara dubu ne, shekara dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.
9 Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma’anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.
10 Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa’an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.
11 Tun da yake duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada,
12 kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su hallaka, dukkan abubuwa kuma da suke a cikinsu, wuta za ta narkar da su.
13 Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin summai da sabuwar ƙasa a inda adalci zai yi zamansa.
14 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama.
15 Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan’uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,
16 yana magana a kan wannan, kamar yadda yake yi a dukan wasiƙunsa, akwai waɗansu abubuwa a cikin masu wuyar fahinta, waɗanda jahilai da marasa kintsuwa suke juya ma’anarsu, kamar yadda suke juya sauren Littattafai, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.
17 Don haka, ya ku ƙaunatatuna, da yake kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.
18 Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!