Jawabin Ubangiji a kan Ammonawa
1 Wannan shi ne abin da Ubangiji ya faɗa akan Ammonawa,
“Isra’ila ba shi da ‘ya’ya ne?
Ko kuwa ba shi da māgada ne?
Me ya sa waɗanda suke bautar Milkom
suka mallaki inda Gad take zama,
Suka zauna a garuruwanta?
2 Domin haka lokaci yana zuwa,
Sa’ad da zan sa mutanen garin
Rabba ta Ammon su ji busar
yaƙi.
Rabba za ta zama kufai,
Za a ƙone ƙauyukanta da wuta,
Sa’an nan Isra’ila zai mallaki
waɗanda suka mallake shi.
Ni Ubangiji na faɗa.
3 “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai ta
zama kufai!
Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, ku
sa tufafin makoki.
Ku yi gudu, kuna kai da kawowa a
cikin garuka,
Gama za a kai Milkom bauta tare da
firistocinsa da wakilansa.
4 Me ya sa kuke taƙama da
ƙarfinku,
Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutane
marasa aminci?
Kun dogara ga dukiyarku,
Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba da
mu?’
5 Ga shi, zan kawo muku razana daga
waɗanda suke kewaye da ku,
Za a kore ku, kowane mutum zai
kama gabansa,
Ba wanda zai tattara ‘yan gudun
hijira.
Ni Ubangiji Allah Mai Runduna
na faɗa.
6 “Amma daga baya zan sa
Ammonawa su wadata kuma,
Ni Ubangiji na faɗa.”
Jawabin Ubangiji a kan Edom
7 Ga abin da Ubangiji Mai Runduna
ya faɗa a kan Edom,
“Ba hikima kuma a cikin Teman?
Shawara ta lalace a wurin masu
basira?
Hikima ta lalace ne?
8 Ku mazaunan Dedan, ku juya, ku
gudu,
Ku ɓuya cikin zurfafa,
Gama zan kawo masifa a kan Isuwa
A lokacin da zan hukunta shi,
9 Idan masu tsinkar ‘ya’yan inabi sun
zo wurinka
Ba za su rage abin kala ba?
Idan kuma ɓarayi sun zo da dare,
Za su ɗauki iyakacin abin da suke so
kurum.
10 Amma na tsiraita Isuwa sarai,
Na buɗe wuraren ɓuyarsa,
Har bai iya ɓoye kansa ba,
An hallakar da mutanen Isuwa
Tare da ‘yan’uwansa da
maƙwabtansa,
Ba wanda ya ragu.
11 Ka bar marayunka, ni zan rayar da
su.
Matanka da mazansu sun mutu,
Sai su dogara gare ni.”
12 Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara’anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!
13 Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la’ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”
14 Irmiya ya ce,
“Na karɓi saƙo daga wurin
Ubangiji.
An aiki jakada a cikin al’ummai
cewa,
‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gāba
da ita,
Ku tasar mata da yaƙi!’
15 Gama ga shi, zan maishe ki
ƙanƙanuwa cikin al’ummai,
Abar raini a wurin mutane.
16 Tsoronki da ake ji da girmankanki
sun ruɗe ki,
Ke da kike zaune a kogon dutse, a
kan tsauni,
Ko da yake kin yi gidanki can sama
kamar gaggafa,
Duk da haka zan komar da ke ƙasa,
Ni Ubangiji na faɗa.”
17 Ubangiji ya ce, “Edom za ta lalace, duk wanda ya bi ta wurin zai gigice, ya yi tsaki saboda dukan masifunta.
18 Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da suke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa.
19 Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?
20 Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su.
21 Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza, za a kuma ji muryar kukansu har a Bahar Maliya.
22 Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”
Jawabin Ubangiji a kan Dimashƙu
23 Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu,
“Hamat da Arfad sun gigice,
Domin sun ji mugun labari,
sun narke saboda yawan damuwa,
Ba za su iya natsuwa ba.
24 Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi,
Ta juya, ta gudu,
Tsoro ya kama ta,
Azaba da baƙin ciki sun kama ta
kamar na naƙuda.
25 Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,
Birnin da take cike da murna?
26 A waccan rana samarinta za su fāɗi a
dandalinta.
Za a hallaka sojojinta duka,
Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
27 Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,
Za ta kuwa cinye fādodin
Ben-hadad.”
Jawabin Ubangiji a kan Kedar da Hazor
28 Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,
“Ku tashi zuwa Kedar,
Ku hallaka mutanen gabas.
29 Za a kwashe alfarwansu da
garkunansu,
Da labulan alfarwansu, da dukan
kayansu.
Za a kuma tafi da raƙumansu,
Za a gaya musu cewa, ‘Razana ta
kewaye ku!’
30 “Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwa
nesa,
Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji na
faɗa,
Gama Nebukadnezzar, Sarkin
Babila, ya shirya muku
maƙarƙashiya,
Ya ƙulla mugun nufi game da ku.
31 Ku tashi ku fāɗa wa al’ummar da take
zama lami lafiya,
Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare,
Suna zama su kaɗai.
32 “Za a washe raƙumansu da
garkunan shanunsu ganima,
Zan watsar da masu yin kwaskwas
ko’ina,
Zan kuma kawo musu masifu daga
kowace fuska,
Ni Ubangiji na faɗa.
33 Hazor za ta zama kufai har abada,
wurin zaman diloli,
Ba wanda zai zauna a ciki, ba wanda
kuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”
Jawabin Ubangiji a kan Elam
34 Maganar da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Elam a farkon sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza.
35 Ubangiji Mai Runduna ya ce,
“Zan karya bakan Elam, inda
ƙarfinta yake.
36 Zan sa iska ta hura a kan Elam daga
kusurwoyi huɗu na samaniya.
Za ta watsar da mutane ko’ina,
Har ba ƙasar da za a rasa mutumin
Elam a ciki.
37 Zan sa mutanen Elam su ji tsoron
maƙiyansu waɗanda suke neman
ransu.
Da zafin fushina zan kawo musu
masifa,
In sa a runtume su da takobi,
Har in ƙare su duka,
Ni Ubangiji na faɗa.
38 Zan kafa gadon sarautata a Elam,
Zan hallaka sarkinta da
shugabanninta.
39 Amma daga baya zan sa Elam kuma
ta wadata.
Ni Ubangiji na faɗa.”