Jawabin Ubangiji a kan Mowab
1 Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya faɗa a kan Mowab,
“Kaiton Nebo, gama ta lalace!
An kunyatar da Kiriyatayim, an ci ta
da yaƙi,
An kunyatar da kagararta, an rushe
ta.
2 Darajar Mowab ta ƙare.
Ana shirya mata maƙarƙashiya a
Heshbon,
‘Bari mu je mu ɓata ta daga zaman
al’umma!’
Ke kuma Madmen za ki yi shiru,
Takobi zai runtume ki.
3 Muryar kuka daga Horonayim tana
cewa,
‘Risɓewa da babbar halaka!’
4 “An hallakar da Mowab,
Ƙanananta suna kuka.
5 Gama a hawan Luhit, za su hau da
kuka,
Gama a gangaren Horonayim,
Suna jin kukan wahalar halaka.
6 Ku gudu don ku tserar da
rayukanku,
Ku gudu kamar jakin jeji.
7 “Kun dogara ga ƙarfinku da
wadatarku,
Amma yanzu za a ci ku da yaƙi,
Kemosh zai tafi bauta
Tare da firistocinsa da
shugabanninsa.
8 Mai hallakarwa zai shiga kowane
gari,
Don haka ba garin da zai tsira.
Kwari da tudu za su lalace,
Ni Ubangiji na faɗa.
9 Ku ba Mowab fikafikai,
Gama za ta tashi ta gudu,
Garuruwanta za su zama kango,
Ba mazauna cikinsu.
10 “La’ananne ne shi wanda yake yin
aikin Ubangiji da ha’inci,
La’ananne ne shi kuma wanda ya
hana wa takobinsa jini.
11 “Tun daga ƙuruciya Mowab tana
zama lami lafiya,
Hankali kwance,
Ba a jujjuya ta daga tulu zuwa tulu
ba,
Ba a taɓa kai ta bauta ba,
Domin haka daɗin ɗanɗanonta bai
rabu da ita ba,
Ƙanshinta kuma bai sāke ba.”
12 Ubangiji ya ce, “Domin haka kwanaki suna zuwa, sa’ad da zai aika da mutane su tuntsurar da tuluna, su zubar da ruwan inabi, su farfasa tulunanta.
13 Sa’an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra’ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.
14 “Don me kake cewa,
‘Mu jarumawa ne, mayaƙan gaske?’
15 Mai hallaka Mowab da garuruwanta
ya taho,
Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sun
gangara mayanka,
Ni sarki, mai suna Ubangiji Mai
Runduna, na faɗa.
16 Masifar Mowab ta kusato,
Halakarta kuma tana gaggabtowa.
17 “Ku yi makoki dominta, ku da kuke
kewaye da ita,
Dukanku da kuka san sunanta, ku
ce,
‘Ƙaƙa sandan sarauta mai iko
Da sanda mai daraja ya karye?’
18 Ku da kuke zaune a Dibon,
Ku sauka daga wurin zamanku mai
daraja,
Ku zauna a busasshiyar ƙasa,
Gama mai hallaka Mowab ya zo ya
yi gab da ku.
Ya riga ya rushe kagararku.
19 Ku mazaunan Arower,
Ku tsaya a kan hanya, ku jira,
Ku tambayi wanda yake gudu
Da wanda yake tserewa,
Abin da ya faru.
20 An kunyatar da Mowab, ta rushe.
Ku yi kuka dominta,
Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab ta
halaka.
21 “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,
22 da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,
23 da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba’almeyon,
24 da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.
25 An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.
26 “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.
27 Kin yi wa mutanen Isra’ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.
28 “Ku mazaunan Mowab, ku bar
garuruwanku,
Ku tafi, ku zauna a kogwanni,
Ku zama kamar kurciya wadda take
yin sheƙarta a bakin kwazazzabo.
29 Mun ji labarin girmankan Mowab,
da ɗaukaka kanta,
Da alfarmarta, da izgilinta,
Tana da girmankai ƙwarai.
30 Ni Ubangiji na san Mowab tana da
girmankai,
Alfarmarta ta banza ce,
Ayyukanta kuma na banza ne.
31 Don haka zan yi kuka saboda
Mowab duka,
Zan kuma yi baƙin ciki saboda
mutanen Kir-heres.
32 Zan yi kuka saboda kurangar inabin
Sibma
Fiye da yadda zan yi kuka saboda
mutanen Yazar.
Rassanku sun haye teku har sun kai
Yazar,
Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan
‘ya’yan itatuwanku da damuna
Da kan amfanin inabinku.
33 An ɗauke farin ciki da murna daga
ƙasa mai albarka ta Mowab,
Na hana ruwan inabi malala daga
wurin matsewarsa,
Ba wanda yake matse shi, yana ihu na
murna,
Ihun da ake yi ba na murna ba ne.
34 “Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe.
35 Zan hana mutanen Mowab miƙa hadayu na ƙonawa a tuddai, da miƙa wa gumakansu sadaka, ni Ubangiji na faɗa.
36 “Zuciyata tana makoki domin Mowab da Kir-heres kamar wanda yake kukan makoki da sarewa saboda wadatarsu ta ƙare.
37 Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.
38 Ba abin da ake yi a bisa kan soraye da dandali na Mowab sai baƙin ciki, gama na farfashe Mowab kamar tulun da ba a so, ni Ubangiji na faɗa.
39 An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda suke kewaye da ita.
40 “Ni Ubangiji na ce,
Wani zai yi firiya da sauri kamar
gaggafa,
Zai shimfiɗa fikafikansa a kan
Mowab.
41 Za a ci garuruwa da kagarai da
yaƙi,
A wannan rana zukatan sojojin
Mowab
Za su zama kamar zuciyar macen da
take naƙuda.
42 Za a hallaka Mowab daga zaman
al’umma,
Domin ta tayar wa Ubangiji.
43 Tsoro, da rami, da tarko suna
jiranku,
Ya mazaunan Mowab,
Ni Ubangiji na faɗa.
44 Wanda ya guje wa tsoro,
Zai fāɗa a rami,
Wanda kuma ya fito daga cikin
rami,
Tarko zai kama shi.
Gama na sa wa Mowab lokacin da
zan hukunta ta,
Ni Ubangiji na faɗa.
45 “A ƙarƙashin inuwar Heshbon ‘yan
gudun hijira suna tsaye ba ƙarfi.
Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon,
Harshen wuta kuma ya fito daga
Sihon,
Ta ƙone goshin Mowab da
ƙoƙwan kai na ‘yan tayarwa.
46 Kaitonku, ya Mowabawa!
Mutanen Kemosh sun lalace,
An kai ‘ya’yanku mata da maza
cikin bauta.
47 “Amma zan komar da mutanen
Mowab nan gaba,
Ni Ubangiji na faɗa.”
Wannan shi ne hukuncin Mowab.