IRM 26

Maƙarƙashiya a Kashe Irmiya

1 A farkon sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2 “Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.

3 Mai yiwuwa ne su ji, har kowa ya juyo ya bar muguwar hanyarsa. Ni ma sai in janye masifar da na yi niyyar aukar musu da ita, saboda mugayen ayyukansu.”

4 Ubangiji ya faɗa wa Irmiya ya ce wa jama’a, “Haka Ubangiji ya ce, idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, ku yi tafiya a dokata wadda na sa a gabanku ba,

5 ku kuma kula da zantuttukan bayina, annabawa, waɗanda na yi ta aiko muku, to, amma ba ku kula ba.

6 Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la’ana ga dukan al’umman duniya.”

7 Firistoci, da annabawa, da dukan jama’a sun ji dukan maganan nan da Irmiya ya faɗa a cikin Haikalin Ubangiji.

8 Sa’ad da Irmiya ya gama faɗar dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa wa dukan jama’a, sai firistoci, da annabawa, da dukan jama’a suka kama shi, suna cewa, “Mutuwa za ka yi!

9 Don me ka yi annabci da sunan Ubangiji, ka ce wannan Haikali zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kufai, ba mazauna a ciki?” Sai jama’a duk suka taru, suka kewaye Irmiya cikin Haikalin Ubangiji.

10 Sa’ad da sarakunan Yahuza suka ji waɗannan al’amura, sai suka fito daga gidan sarki zuwa Haikalin Ubangiji, suka zauna a bakin Sabuwar Ƙofa ta Haikalin Ubangiji.

11 Sai firistoci da annabawa suka faɗa wa sarakunan nan da jama’a duka, suka ce, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa, gama ya yi annabci gāba da wannan birni kamar yadda kuka ji da kunnuwanku.”

12 Sa’an nan sai Irmiya ya yi magana da dukan sarakuna da dukan jama’a, ya ce, “Ubangiji ne ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan Haikali da wannan birni, da irin maganar da kuka ji.

13 Saboda haka yanzu sai ku gyara al’amuranku da ayyukanku, ku yi biyayya kuma da muryar Ubangiji Allahnku. Ubangiji kuwa zai janye masifar da ya hurta gāba da ku.

14 Amma ni kaina kuwa a hannunku nake, sai ku yi mini yadda kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku.

15 Ku tabbata dai, idan kuka kashe ni, za ku jawo hakkin jinin marar laifi a kanku da a kan wannan birni da mazauna a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”

16 Sarakuna kuwa da dukan jama’a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

17 Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama’a,

18 “Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa,

‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna

ya ce,

Za a nome Sihiyona kamar gona,

Urushalima kuwa za ta zama tsibin

juji,

Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama

kurmi.’

19 Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”

20 Akwai wani mutum kuma wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji. Sunansa Uriya ɗan Shemaiya mutumin Kiriyat-yeyarim. Ya yi annabci gāba da birnin nan da ƙasan nan da magana irin ta Irmiya.

21 Sa’ad da sarki Yehoyakim, da dukan jarumawansa, da dukan sarakunansa suka ji maganarsa, sai sarki yana so ya kashe shi, amma sa’ad da Uriya ya ji, sai ya ji tsoro, ya gudu ya tsere zuwa Masar.

22 Sa’an nan sai sarki Yehoyakim ya aiki waɗansu mutane zuwa Masar, wato Elnatan ɗan Akbor da waɗansu tare da shi.

23 Suka kamo Uriya daga Masar suka kawo shi wurin sarki Yehoyakim, sai ya sa aka kashe shi da takobi, aka binne gawarsa a makabartar talakawa.

24 Amma Ahikam ɗan Shafan yana tare da Irmiya, saboda haka ba a bashe shi ga mutane don su kashe shi ba.