Saɓani Tsakanin Irmiya da Fashur Firist
1 Sa’ad da Fashur, firist, ɗan Immer, shugaban Haikalin Ubangiji ya ji Irmiya yana annabci a kan waɗannan abubuwa,
2 sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka, aka kuma sa shi cikin turu a ƙofar Biliyaminu, a Haikalin Ubangiji.
3 Kashegari sa’ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska.
4 Haka Ubangiji ya ce, ‘Ga shi, zan maishe ka abin tsoro ga kai kanka, da dukan abokanka. Abokan gābansu za su kashe su da takobi a kan idonka. Zan ba da dukan Yahuza a hannun Sarkin Babila, shi kuwa zai kwashe waɗansu ya kai bautar talala a Babila, ya kuma kashe waɗansu da takobi.
5 Banda haka kuma zan ba da dukan dukiyar wannan birni, da dukan ribarsa, da dukan abubuwa masu tamani, da dukan dukiyar sarakunan Yahuza, ga abokan gābansu, waɗanda za su washe su, su kama su, su kai Babila.
6 Kai kuma, Fashur, da dukan waɗanda suke a gidanka, za ku tafi bauta a Babila, za ku shiga Babila, a can za ku mutu, a can za a binne ku, kai da abokanka waɗanda ka yi wa annabcin ƙarya.’ ”
Kukan Irmiya
7 “Ya Ubangiji ka ruɗe ni, na kuwa
ruɗu,
Ka fi ni ƙarfi, ka kuwa rinjaye ni.
Na zama abin dariya dukan yini,
Kowa yana ta yi mini ba’a.
8 Duk lokacin da zan yi magana,
Nakan ta da murya in yi magana da
ƙarfi cewa,
‘Hargitsi da hallakarwa!’
Gama saboda maganar Ubangiji na
zama abin zargi,
Da abin ba’a dukan yini.
9 Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangiji
ba,
Ban zan ƙara yin magana da sunansa
ba,’
Sai in ji damuwa a zuciyata,
An kulle ta a ƙasusuwana,
Na gaji da danne ta a cikina,
Ba zan iya jurewa ba.
10 Na ji mutane da yawa suna sa mini
laƙabi cewa,
‘Razana ta kowace fuska,’
Suna cewa, ‘Mu la’anta shi!
Mu la’anta shi!’
Har ma da abokaina shaƙiƙai
Suna jira su ga fāɗuwata.
Suka ce, ‘Watakila a ruɗe shi,
Sa’an nan ma iya rinjayarsa
Mu ɗauki fansa a kansa.’
11 Amma Ubangiji kana tare da ni
Kamar jarumi mai bantsoro,
Don haka masu tsananta mini za su
yi tuntuɓe,
Ba za su rinjaye ni ba.
Za su sha kunya ƙwarai,
Gama ba za su yi nasara ba.
Ba za a manta da su ba.
12 Ya Ubangiji Mai Runduna, mai
gwada adali,
Mai ganin zuciya duk da tunani,
Ka sa in ga sakayyar da za ka yi
musu,
Gama a gare ka nake kawo
ƙarata.”
13 Ku raira waƙa ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji!
Gama ya kuɓutar da ran mabukaci
daga hannun mugaye.
14 La’ananniya ce ranar da aka haife
ni,
Kada ranar da uwata ta haife ni ta yi
albarka!
15 La’ananne ne mutum da ya kai wa
mahaifina labari
Cewa, “An haifa maka ɗa,” don ya
sa shi farin ciki.
16 Bari wannan mutum ya zama kamar
biranen da Ubangiji ya kaɓantar
ba tausayi.
Bari ya ji kuka da safe,
Da rana kuma ya ji gangamin yaƙi,
17 Domin bai kashe ni tun ina ciki ba.
Da ma cikin uwata ya zama mini
kabari,
In yi ta kwanciya a ciki har abada.
18 Me ya sa na fito daga cikin mahaifa,
Don in ga wahala da baƙin ciki,
Don kwanakin raina su ƙare da
kunya?