Hakkin Aure
1 Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,
2 don ganin tsarkakakken halinku da kuma ladabinku.
3 Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso, da kayan zinariya, ko tufafi masu ƙawa,
4 sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali’u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.
5 Don dā ma haka tsarkakan mata masu dogara ga Allah suka yi ado, suka bi mazansu,
6 kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma ‘ya’yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.
7 Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa’a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu’a tare.
Shan Wuya don Adalci
8 Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar ‘yan’uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali’u.
9 Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.
10 Domin,
“Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri,
Sai ya kame bakinsa daga ɓarna,
Ya kuma hana shi maganar yaudara.
11 Ya rabu da mugunta,
ya kama nagarta,
Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.
12 Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci,
Yana kuma sauraron roƙonsu.
Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”
13 To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari?
14 Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu.
15 Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali’u da bangirma.
16 Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.
17 Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da yake nagari, in haka nufin Allah ne, da a sha don yin abin da ba daidai ba.
18 Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.
19 Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela,
20 wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa’ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.
21 Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,
22 wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala’iku da manyan mala’iku da masu iko suna binsa.