IRM 11

An Ta da Alkawari

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya cewa,

2 “Ka ji maganar wannan alkawari, sa’an nan ka faɗa wa mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.

3 Ka faɗa musu cewa, ‘In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, la’ananne ne wanda bai kula da maganar alkawarin nan ba.

4 Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.

5 Sa’an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ”

Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”

6 Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuza da titunan Urushalima duka, cewa su ji maganar alkawarin nan, su aikata.

7 Lokacin da na fito da kakanninsu daga ƙasar Masar na faɗakar da su musamman, na yi ta faɗakar da su har wannan rana, ina cewa, ‘Ku yi biyayya da maganata.’

8 Amma duk da haka ba su yi biyayya ba, ba su kuma kasa kunne ba. Kowa ya bi tattaurar zuciyarsa mai mugunta. Domin haka na kawo musu dukan maganar alkawarin nan wanda na umarce su su yi, amma ba su yi ba.”

9 Ubangiji ya kuma ce mini, “Akwai tawaye a cikin mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima.

10 Sun koma a kan laifofin kakanninsu, waɗanda suka ƙi jin maganata, suka bi gumakansu don su bauta musu, jama’ar Isra’ila da na Yahuza sun ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu.

11 Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.

12 Sa’an nan biranen Yahuza da mazaunan Urushalima za su tafi, su yi kuka ga gumaka waɗanda suka ƙona musu turare, amma ba za su iya cetonsu a lokacin wahalarsu ba.

13 Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba’al turare ne.’

14 Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu’a. Kada ka yi kuka ko addu’a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”

15 Ubangiji ya ce, “Wane iko ƙaunatacciyata take da shi cikin Haikalina, da ya ke ta aikata mugayen ayyuka? Ko alkawarai da naman hadayu za su iya kawar miki da ƙaddararki, har da za ki yi taƙama?

16 Dā na kira ki itacen zaitun mai duhuwa, kyakkyawa, mai kyawawan ‘ya’ya, amma da ƙugin babbar iska za a cinna miki wuta, za ta kuwa cinye rassanki.”

17 Ubangiji Mai Runduna, wanda ya dasa ku, ya hurta masifar da za ta same ku saboda muguntar da mutanen Isra’ila da na Yahuza suka yi, suka tsokane ni in yi fushi saboda suna ƙona wa Ba’al turare.

An Shirya Maƙarƙashiya don a Kashe Irmiya

18 Ubangiji ya sanasshe ni,

Na kuwa sani,

Sa’an nan ya nuna mini mugayen

ayyukansu.

19 Amma ina kama da lafiyayyen ɗan

rago,

Wanda aka ja zuwa mayanka,

Ashe, ni suke ƙulla wa munafuncin!

Ni kuwa ban sani ba, da suke cewa,

“Bari mu lalatar da itacen duk da

‘ya’yansa.

Bari mu datse shi daga ƙasar masu

rai,

Har da ba za a ƙara tunawa da

sunansa ba.”

20 Amma ya Ubangiji Mai Runduna,

mai shari’ar adalci,

Kakan gwada zuciya da tunani,

Ka yarda mini in ga sakayyar da za

ka yi mini a kansu,

Gama a gare ka na danƙa

maganata.

21 Saboda haka ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka, da suka ce, “Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji, in ba haka ba, da hannunmu za mu kashe ka.”

22 Domin haka ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ga shi kuwa, zan hukunta su, za a kashe samarinsu da takobi, ‘ya’yansu mata da maza, yunwa za ta kashe su.

23 Ba wanda zai ragu daga cikin mutanen Anatot, gama zan kawo wa mutanen Anatot masifa, a shekarar hukuncinsu.”