Rayayyen Dutse da Kabila Tsattsarka
1 Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha’inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe.
2 Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,
3 in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.
4 Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah.
5 Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,
6 Domin a tabbace yake a Nassi cewa,
“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,
Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
7 A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to,
“Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”
8 Da kuma,
“Dutsen sa tuntuɓe,
Da fā na sa faɗuwa.”
Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.
9 Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al’umma, jama’ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al’amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
10 Dā ba jama’a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama’ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.
Ku yi Zaman Bayin Allah
11 Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha’awace-sha’awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.
12 Ku yi halin yabo a cikin al’ummai, don duk sa’ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
13 Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba,
14 ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a’aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki.
15 Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari.
16 Ku yi zaman ‘yanci, sai dai kada ku fake a bayan ‘yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.
17 Ku girmama kowa, ku ƙaunaci ‘yan’uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
Koyi da Wahalar Almasihu
18 Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai.
19 Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.
20 To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.
21 Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.
22 Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba.
23 Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari’ar adalci.
24 Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.
25 A dā kun ɓăce kamar tumaki, amma a yanzu kun dawo ga Makiyayi, wato mai kula da rayukanku.