Hukuncin Ubangiji da Wadatar Sihiyona
1 Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?
2 Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali’u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.
3 “Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu’a ga gumaka. Suna jin daɗin al’amuran banƙyama a lokacin yin sujada.
4 Saboda haka zan aukar musu da masifa, ainihin abin da suke jin tsoro, gama ba wanda ya amsa sa’ad da na yi kira, ko ya kasa kunne sa’ad da na yi magana. Suka zaɓa su yi mini rashin biyayya, su kuma aikata mugunta.”
5 Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga ‘yan’uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba’a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!
6 Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!
7 “Tsattsarkan birnina yana kama da uwa wadda ta haifi ɗa, ba tare da naƙuda ba.
8 Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al’umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al’umma.
9 Kada ku zaci zan kawo jama’ata a wurin haihuwa in kuma hana ta haihuwa.” Ubangiji ne ya faɗa.
10 Ku yi murna tare da Urushalima
Ku yi farin ciki tare da ita,
Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan!
Ku yi murna tare da ita yanzu,
Dukanku da kuka yi makoki dominta!
11 Za ku ji daɗin wadatarta,
Kamar yaro a ƙirjin mamarsa.
12 Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al’ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.
13 Zan ta’azantar da ku a Urushalima, kamar yadda uwa take ta’azantar da ɗanta.
14 Sa’ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”
15 Ubangiji zai zo da wuta. Zai hau a kan fikafikan hadiri, domin ya hukunta waɗanda yake fushi da su.
16 Zai hukunta dukan mutanen duniya da wuta da takobi, waɗanda ya same su da laifi, za su kuwa mutu.
17 Ubangiji ya ce, “Ƙarshe ya kusa ga waɗanda suka tsabtace kansu domin sujadar arna, suka kuma yi jerin gwano zuwa ɗakin tsafi a lambu, inda suka ci naman alade da na ɓera, da waɗansu abinci masu banƙyama.
18 Na san tunaninsu da ayyukansu. Ina zuwa domin in tattara jama’ar dukan al’ummai. Sa’ad da suka tattaru, za su ga abin da ikona zai yi,
19 su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu.
“Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al’ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al’ummai.
20 Za su taho da ‘yan ƙasarku daga al’ummai, su kawo mini su kyauta. Za su zo da su a tsattsarkan dutsena, wato Urushalima, za su kawo su a kan dawakai, da alfadarai, da raƙuma, da cikin karusai, kamar dai yadda Isra’ilawa suke kawo hadaya ta hatsi a Haikali cikin tsabtatattun ƙore.
21 Zan sa waɗansu su zama firistoci da Lawiyawa.”
22 Ubangiji ya ce, “Kamar yadda sabuwar duniya da sabon sararin sama za su tabbata ta wurin ikona, haka zuriyarku da sunanku za su tabbata.
23 A kowane bikin amaryar wata, da kowace ranar Asabar, jama’ar kowace al’umma za su zo su yi mini sujada a nan cikin Urushalima.
24 Sa’ad da suke tafiya, za su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa. Tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, wutar da take ƙona su kuma ba za ta taɓa mutuwa ba. Dukan mutane za su ji ƙyamarsu.”