Ranar Ramawa ta Ubangiji
1 Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa?
Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.
2 Me ya sa tufafinsa suke da ja haka, kamar na mutumin da ya tattake ‘ya’yan inabi domin ya sami ruwan inabi?
3 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na tattake al’ummai kamar ‘ya’yan inabi, ba kuwa wanda ya taimake ni. Na tattake su cikin fushina, jininsu kuwa ya fantsamar wa dukan tufafina.
4 Na ga lokacin da zan fanshi mutanena ya yi, lokaci ne da zan hukunta wa abokan gābansu.
5 Na yi mamaki sa’ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.
6 Da fushina na tattake dukan sauran al’umma, na farfashe su. Na kwararar da jinin ransu a ƙasa.”
Alherin Ubangiji ga Isra’ila
7 Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa,
Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana.
Ya sa wa jama’ar Isra’ila albarka mai yawa,
Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.
8 Ubangiji ya ce, “Su mutanena ne, ba za su ruɗe ni ba.” Saboda haka kuwa ya cece su
9 daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala’ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,
10 amma suka i masa tayarwa, suka cika shi da ɓacin rai. Saboda haka Ubangiji ya yi gāba da su, ya kuwa yi yaƙi da su.
11 Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama’arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?
12 Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al’amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama’arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”
13 Sa’ad da Ubangiji ya bi da su ta ruwa mai zurfi, suka taka kamar ingarmun dawakai, ba su ko yi tuntuɓe ba.
14 Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.
Addu’ar Neman Jinƙai da Taimako
15 Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.
16 Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe.
17 Don me ka bari muka ɓata daga al’amuranka? Don me ka bari muka taurare, har muka bar binka? Ka komo, domin darajar waɗanda suke bauta maka, domin kuma mutanen da suke naka ne a koyaushe.
18 Abokan gabanmu sun kusa su kori mutanenka gaba ɗaya sun kuma tattake Haikalinka.
19 Mun zama kamar ba ka taɓa zama mai mulkinmu ba, kamar mu kuma ba mu taɓa zama mutanenka ba.