1 BIT 1

Gaisuwa

1 Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,

2 su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.

Rayayyiyar Bege

3 Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

4 mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,

5 wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.

6 A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.

7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.

8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,

9 kuna samun ceton rayukanku, ta wurin sakamakon bangaskiyarku.

10 Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto,

11 suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa’ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.

12 An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala’iku suke ɗokin gani.

Kira a Yi Zaman Tsarki

13 Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.

14 Ku yi zaman ‘ya’ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha’awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku.

15 Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al’amuranku.

16 Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”

17 Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu’a, shi da yake yi wa kowa shari’a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.

18 Domin kun sani an fanshe ku ne daga al’adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba,

19 sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo.

20 An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe.

21 To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

22 Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga ‘yan’uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.

23 Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.

24 Domin

“Duk ɗan adam kamar ciyawa yake,

Duk darajarsa kamar furen ciyawa take,

Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,

25 Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,”

Ita ce maganar bishara da aka yi muku.