1 Adalin mutum yakan mutu, amma ba wanda ya kula. An kwashe mutanen kirki ba kuwa wanda ya kula, an tsame adali daga cikin bala’i.
2 Ya shiga da salama yana hutawa a kabarinsa, shi wanda ya yi tafiya da adalci.
3 Amma ku ku matso nan kusa, ku ‘ya’ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinaci da karuwa.
4 Wa kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke wage baki, kuna zaro harshe? Ashe, ku ba ‘ya’yan masu laifi ba ne, zuriyar marikita,
5 ku da muguwar sha’awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe ‘ya’yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?
6 Rabonku yana cikin duwatsu masu sulɓi na cikin kwari. A gare su kuka kwarara hadaya ta sha, kuka kawo hadaya ta gari. Kuna tsammani zan ji daɗin waɗannan al’amura?
7 A kan dogayen duwatsu masu tsayi kuka sa gadonku. A can kuka haura don ku miƙa hadaya.
8 A bayan ƙofa da madogaran ƙofa kuka kafa gumakanku. Kun rabu da ni, kun kware gadonku, kuna hau kun fāɗaɗa shi, kuka ƙulla yarjejeniya tsakaninku da su. Kuna ƙaunar gadonsu, kun dubi tsiraici.
9 Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira.
10 Kun damu saboda nisan hanyarku, amma ba ku ce, “Ba shi da wani amfani ba.” Ƙarfinku ya sake sabunta ranku, don haka ba ku suma ba.
11 Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba?
12 Zan ba da labarin adalcinku da ayyukanku, amma ba za su taimake ku ba.
13 Sa’ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.”
Taimakon Allah da Warkarwa
14 Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama’ata!”
15 Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali’u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali’u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.
16 Ba zan yi ta gāba da ku, ko in yi ta fushi da ku har abada ba. Gama ruhu zai yi suma a gabana, da numfashin su waɗanda na halitta.
17 Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.
18 “Na ga al’amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta’azantar da su tare da masu makoki.
19 Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su.
20 Amma mugaye suna kama da tumbatsar teku, gama ba ta iya natsuwa. Ruwanta kuma yana tumbatsa, ya gurɓace, ya ƙazantu.”
21 Allah ya ce, “Ba salama ga mugaye.”