Allah Ya Nuna Jinƙai ga Kowa
1 Ubangiji ya ce,
“Duk mai jin ƙishi ya zo,
Ga ruwa a nan!
Ku da ba ku da kuɗi ku zo,
Ku sayi hatsi ku ci!
Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara,
Ba za ku biya kome ba!
2 Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba?
Don me za ku ɓad da albashinku, amma kuna ta shan yunwa?
Ku kasa kunne gare ni, ku yi abin da na faɗa,
Za ku sha daɗin abinci mafi kyau duka.
3 “Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni,
Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai!
Zan yi tabbataccen alkawari da ku,
Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.
4 Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al’ummai,
Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.
5 Yanzu kuwa za ku kira al’ummai, baƙi,
Dā ba su kuwa san ku ba, ko da rana ɗaya,
Amma yanzu za su sheƙo a guje domin su haɗa kai da ku!
Ni, Ubangiji Allahnku, Allah Mai Tsarki na Isra’ila,
Zan sa dukan wannan ya faru,
Zan ba ku girma da daraja.”
6 Ku juyo wurin Ubangiji, ku yi addu’a gare shi,
Yanzu da yake kusa.
7 Bari mugaye su bar irin al’amuransu,
Su sāke irin tunaninsu.
Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu,
Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.
8 Ubangiji ya ce,
“Tunanina ba kamar irin naku ba ne,
Al’amurana kuma dabam suke da naku.
9 Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
Haka al’amurana da tunanina suke nesa da naku.
10 “Maganata kamar dusar ƙanƙara take,
Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya.
Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba,
Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.
11 To, haka maganar da na faɗa take,
Ba ta kāsa cika abin da na shirya mata,
Za ta yi kowane abin da na aike ta ta yi.
12 “Za ku fita daga cikin Babila da murna,
Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama.
Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa,
Itatuwa za su yi ta sowa don murna!
13 Itacen fir zai tsiro a wurin da sarƙaƙƙiya take yanzu,
Itacen ci-zaƙi zai tsiro a maimakon ƙayayuwa.
Wannan zai zama alamar da za ta kasance har abada,
Matuni ne na abin da ni, Ubangiji, na yi.”