Allah Zai Ceci Urushalima
1 Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma!
Birni mai tsarki na Allah,
Ki yafa wa kanki jamali!
Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.
2 Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima!
Ki tashi daga cikin ƙura,
Ki hau gadon sarautarki.
Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke,
Ke kamammiyar jama’ar Sihiyona!
3 Ubangiji ya ce wa jama’arsa,
“Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba,
Amma ga shi, kuka zama bayi.
Ba za a biya kuɗin fansa domin a ‘yantar da ku ba,
Amma, ga shi, za a ‘yantar da ku.
4 Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar,
Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.
5 Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila,
Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili.
Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya,
Suna ta nuna mini raini.
6 Amma zuwa gaba za ku sani
Ni ne Allah, wanda na yi magana da ku.”
7 Me ya fi wannan kyau?
A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu,
Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.
Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,
“Allahnki sarki ne!”
8 Waɗanda suke tsaron birni suna sowa,
Suna sowa tare saboda murna!
Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!
9 Ku ɓarke da sowar murna,
Ku kufan Urushalima!
Ubangiji ya ta’azantar da jama’arsa,
Ya fanshi birninsa.
10 Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki,
Ya ceci jama’arsa,
Dukan duniya kuwa ta gani.
11 Ku fita, ku bar Babila
Ku dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji!
Kada ku taɓa abin da aka hana,
Ku kiyaye kanku da tsarki,
Ku fita ku bar birnin.
12 A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba,
Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba!
Ubangiji Allah ne zai bishe ku,
Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.
Bawan Ubangiji Mai Shan Wuya
13 Ubangiji ya ce,
“Bawana zai yi nasara a aikinsa,
Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.
14 Mutane da yawa suka gigice sa’ad da suka gan shi,
Ya munana har ya fita kamannin mutum.
15 Amma yanzu al’ummai da yawa za su yi mamaki a kansa,
Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki.
Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”