Annabci a kan Sababbin Abubuwa
1 Ku kasa kunne, ya jama’ar Isra’ila,
Ku da kuke zuriyar Yahuza.
Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji,
Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra’ila,
Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.
2 Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa
Ku ne mazaunan birni mai tsarki,
Kuna kuma dogara ga Allah na Isra’ila,
Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.
3 Ubangiji ya ce wa Isra’ila,
“Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru,
Sa’an nan na sa ya faru ba labari!
4 Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne,
Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.
5 Tuntuni na yi faɗi a kan makomarku,
Na hurta abubuwa tun kafin su faru,
Domin kada ku ɗauka cewa gumakanku ne suka yi su,
Siffofinku ne kuma suka sa abin ya zama haka.
6 “Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu,
Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce.
Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo,
Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.
7 Yanzu ne kaɗai nake sawa su faru,
Ba wani abu makamancin wannan da ya faru a baya.
Da ya faru, da za ku ɗauka cewa kun san kome a kansa.
8 Na sani ba za a iya gaskata ku ba,
Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa.
Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan,
Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.
9 “Saboda mutane su yi yabon sunana
Shi ya sa nake danne fushina,
Ina kuma ɓoye shi, kada in hallaka ku.
10 Na gwada ku da wutar wahala,
Kamar yadda ake tace azurfa a tanda,
Amma na tarar ba ku da amfani.
11 Abin da na yi, na yi shi don kaina ne,
Ba zan bari a rasa girmama sunana ba,
Ko kuwa wani dabam ya sami ɗaukaka
Wadda take tawa ce, ni kaɗai.”
Ubangiji Zai Fanshi Isra’ila
12 “Ku kasa kunne gare ni, ya Isra’ila, jama’ar da na kira!
Ni ne Allah, farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici!
13 Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya,
Ya kuma shimfiɗa sammai.
Lokacin da na kira duniya da sararin sama,
Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!
14 “Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne!
Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba,
Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila,
Zai yi abin da na umarce shi.
15 Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi,
Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.
16 “Yanzu fa, sai ku matso kusa da ni,
Ku ji abin da nake faɗa.
Tun da farko na yi magana da ku a fili,
A koyaushe nakan cika maganata.”
(Yanzu Ubangiji Allah ya ba ni iko, ya kuwa aike ni.)
17 Allah Mai Tsarki na Isra’ila,
Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce,
“Ni ne Ubangiji Allahnku,
Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku,
Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.
18 “Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum!
Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku
Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba!
Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa
Da suke bugowa zuwa gāɓa.
19 Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi,
Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”
20 Ku fita daga Babila, ku tafi a sake!
Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko’ina,
“Ubangiji ya fanshi bawansa Isra’ila!”
21 Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi,
Ba su sha wahalar ƙishi ba.
Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu,
Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.
22 Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”