Ubangiji kaɗai ne Mai Fansa
1 Ya Isra’ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce,
“Kada ku ji tsoro, na fanshe ku.
Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.
2 Sa’ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi,
Zan kasance tare da ku,
Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba.
Sa’ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba,
Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
3 Gama ni ne Ubangiji Allahnku,
Allah Mai Tsarki na Isra’ila, wanda ya cece ku.
Zan ba da Masar, da Habasha, da Seba
Ga Sairus domin fansarku.
4 Zan ba da dukan al’ummai don in ceci ranku,
Gama kuna da daraja a gare ni,
Gama na ba ku girma, ina kuma ƙaunarku.
5 Kada ku ji tsoro, ina tare da ku!
“Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa,
Zan kawo jama’arku zuwa gida.
6 Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi,
Arewa kuma kada su riƙe su a can.
Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe,
Daga kowane sashi na duniya.
7 Su mutanena ne, na kaina,
Na kuwa halicce su don su girmama ni.”
8 Allah ya ce,
“Kirawo mutanena a ɗakin shari’a.
Suna da idanu, amma makafi ne,
Suna da kunnuwa, amma kurame ne!
9 Kirawo sauran al’umma, su zo ga shari’a.
A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba?
A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu?
Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsu
Don su tabbatar daidai suke,
Su shaida gaskiyar maganganunsu.
10 “Ya jama’ar Isra’ila, ku ne shaiduna,
Na zaɓe ku al’umma, baiwata,
Domin ku san ni, ku gaskata ni,
Ku kuma fahimta, ni kaɗai ne Allah.
In banda ni ba wani Allah,
Ba a taɓa yin wani ba,
Ba kuwa za a yi ba.
11 “Ni kaɗai ne Ubangiji,
Ni kaɗai ne wanda yake da ikon yin ceto.
12 Na faɗi abin da zai faru
Sa’an nan na zo domin taimakonku.
Ba wani gunkin da ya taɓa yin haka,
Ku ne shaiduna.
13 Ni ne Allah, haka kuwa nake tutur,
Ba wanda zai iya tserewa daga ikona,
Ba mai iya sāke abin da na riga na yi.”
Za a Hallaka Babila
14 Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce,
“Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila,
Zan rushe ƙofofin birni,
Sowar mutanen birnin za ta zama kuka.
15 Ni ne Ubangiji, Allahnku Mai Tsarki na Isra’ila,
Ni na halicce ku, ni ne kuma sarkinku.”
16 Tuntuni Ubangiji ya shirya hanya ta cikin teku,
Da turba kuma a cikin ruwa.
17 Ya bi da manyan sojoji zuwa hallaka,
Sojojin karusai da na dawakai.
Sun faɗi warwar, ba za su ƙara tashi ba,
An hure su kamar ‘yar wutar fitila!
18 Amma Ubangiji ya ce,
“Kada ku maƙale wa abubuwan da suka wuce,
Ko ku riƙa tunanin abin da ya faru tuntuni.
19 Ku duba abin da nake shirin yi.
Yana ta faruwa ma, kuna iya ganinsa yanzu!
Zan yi hanya a cikin jeji,
In kuma ba ku rafuffukan ruwa a can.
20 Har da namomin jeji za su girmama ni,
Diloli da jiminai za su yi yabona
Sa’ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada,
Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.
21 Su ne mutanen da na yi domin kaina,
Za su raira yabbaina!”
22 Ubangiji ya ce,
“Amma ba ni kuka yi wa sujada ba,
Kun gaji da ni, ya Isra’ila.
23 Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba,
Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba.
Ban nawaita muku da neman hadayu ba,
Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.
24 Ba ku sayi turare domina ba,
Ko ku gamshe ni da kitsen dabbobinku.
Maimakon haka, sai kuka nawaita mini da zunubanku,
Kuka gajiyar da ni da abubuwan da kuke aikatawa da ba daidai ba.
25 Duk da haka, ni ne Allah wanda ya shafe zunubanku,
Na kuwa yi haka saboda yadda nake.
Ba zan ƙara tunawa da zunubanku kuma ba.
26 “Bari mu tafi ɗakin shari’a, ku kawo ƙararrakinku.
Ku gabatar da matsalarku don a tabbatar kuna da gaskiya!
27 Kakanninku na farko sun yi zunubi,
Manyanku sun yi mini laifi.
28 Zan musunci masu mulkin tsattsarkan masujadai,
Saboda haka zan jawo wa Isra’ila hallaka,
Zan bari a la’anta mutanena su sha zagi!”